Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Na Ƙara Samun Galaba A Kan ’Yan Ta’adda a Katsina, Sun Kwato Dabbobi 529

Dakarun sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin Rundunar 17 Brigade a Katsina sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 da ’yan ta’adda suka sace, bayan g...

Dakarun sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin Rundunar 17 Brigade a Katsina sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 da ’yan ta’adda suka sace, bayan gumurzu da aka yi da su a Kafur, Jihar Katsina. Rundunar ta ce samamen ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da suka nuna motsin ’yan ta’adda a yankin Kasuwan Sabo.

A cewar Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Kyaftin Abayomi Adisa, dakarun FOB Malumfashi ƙarƙashin jagorancin Kwamandan sansanin, Laftanar Kanar M.M. Isa, sun kai samamen a ranar 7 ga Fabrairu, 2026, kan wasu ’yan ta’adda da ake zargin sun shigo daga Jihar Zamfara. Rahotanni sun nuna cewa an danganta jagorancin gungun yan ta’addan da Idi Abasu Aiki, wanda ake zargin ɗan’uwan fitaccen jagoran ’yan bindiga Ado Aliero ne.

Da sojojin suka iso, ’yan ta’addan sun buɗe wuta, amma dakarun sun mayar da martani da ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa dazuzzuka tare da barin wasu daga cikin dabbobin da suka sace. Sojojin sun ci gaba da binsu tsakanin Burdugau da Unguwan Matau a Malumfashi, inda ’yan ta’addan suka ƙara watsar da sauran dabbobin.

Jimilla, an ƙwato shanu 290, tumaki 238, jaki 1, da kuma babur 1, duk da cewa shanu 14 sun mutu yayin musayar wuta bayan da ’yan ta’addan suka yi amfani da su a matsayin garkuwa. Rundunar ta ce babu wani soja da ya jikkata. An miƙa dabbobin ga hukumomin da abin ya shafa domin tantancewa da mayar da su ga masu su, tare da yabon jarumtaka da ƙwarewar dakarun daga GOC 8 Division, Manjo Janar Paul Koughna, wanda ya tabbatar da ci gaba da tsaurara farmaki domin tabbatar da tsaro a yankin.

 

No comments