A yau Alhamis 7 ga watan Mayu ne, Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ƙaddamar da neman takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a huku...
A yau Alhamis 7 ga watan Mayu ne, Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ƙaddamar da neman takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukumance ga uwar jam’iyyar APC ta ƙasa.
A wani gagarumin taro da aka gudanar a ɗakin taro na *Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre,* Mataimakin ya jagoranci mambobin jam’iyyar da suka haɗa da gwamnoni, da 'yan majalisun tarayya, da sauran masu madafun iko na da da na yanzu, inda ya miƙa fom ɗin neman takarar ga Shugabannin jam'iyyar a wani mataki na nuna goyon bayan masu madafun iko ga ƙudurin sake zaben shugaba Tinubu zango na biyu.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan miƙa fom ɗin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya bayyana shugaban a matsayin jagora mai juriya wanda ya yi nasarar Jan ragamar Nijeriya zuwa tudun-mun-tsira a yayin da guguwar matsalolin tattalin arziki ta so yin awon gaba da ita.
Kashim ya kafa hujja da ajandar "Renewed Hope" a matsayin babban dalilin cancantar Shugaba Tinubu ga zagaye na biyu inda ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo sun fara samar da sakamako mai kyau, duk da tsaurin da suka zo da shi a karon farko.
"Ƙalubalen shekarun da suka gabata ba su raunana Shugaba Tinubu ba; maimakon haka ma sai kara masa kwarewa da suka yi," in ji Shettima, inda ya ci gaba da cewa
"Wannan gwarzantaka da ƙwarewa da ya kara ne ya sa mu ke fatan kara masa wata dama"
A nata bangaren, uwar jam’iyyar ta kasa ta nuna cikakken goyon bayanta ga takarar, inda
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya karbi takardun takarar, ya ce ayyukan shugaba Tinubu a sassa daban-daban na farfado da ƙasar sun sa sake zaben nasa ya zama dole.
Yilwatda ya yi nuni da kyautatuwar tattalin arziki da karuwar kwarin gwiwar kasashen duniya ga makomar Najeriya a matsayin hujjojin da jam’iyyar ta dogara da su wajen amincewa da takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shi ma shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yaba da garambawul din na shugaban Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin harsashin farfadowar kasa mai dorewa.
Ita ma kungiyar Gwamnonin APC ta bakin Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda gwamnoni 12 suka rufa wa baya ta nuna goyon baya na bai-daya ga takarar
Gwamnonin da suka halarci taron su ne na jihohin Plateau, Ogun, Niger, Kaduna, Ondo, Katsina, Borno, Cross River, Taraba, Yobe, Nasarawa, Zamfara da Bayelsa.
A yanzu dai mika tikitin takarar a hukumance ya kawo karshen rade-raden da ake yi game da aniyar shugaban ta neman wa'adin Mulki na biyu kamar yadda ta bayyana irin hadin kan Shugabanni na bai daya da ake dakon gani a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.
Shugabannin jam’iyyar sun yi kira ga mambobinsu da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu don "kare fatan Najeriya.".










No comments