Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NiMet Ta Yi Gargaɗin Samun Tsananin Zafi A Wasu Jihohin Arewacin Nijeriya

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi gargaɗin cewa za a samu matsanancin yanayin zafi a ƙasar, inda ta ce hakan zai iya kai wasu...




Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi gargaɗin cewa za a samu matsanancin yanayin zafi a ƙasar, inda ta ce hakan zai iya kai wasu ga shiga yanayin galabaita saboda zafin a wasu sassan ƙasar.

A wata sanarwa da ta fitar a shafukanta, NiMet ta ce yanayin zafin zai fi shafar jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da jihohin Neja da Kebbi da Kano da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Yobe da Jigawa da Bauchi da Gombe da Borno da kuma Adamawa.

A cewar sanarwar, akwai yiwuwar wasu jihohin ma da ba a ambata ba su samu ƙaruwar yanayin na zafi.

A hasashen ta, yanayin zafin zai iya kai wa maki 40 zuwa 45 a ma'aunin salshiyas a arewacin ƙasar, yayin da tsakiyar ƙasar kuma zai kai tsakanin maki 35 zuwa 38 a ma'aunin salshiyas, a Kudancin ƙasar kuma yanayin na iya kai wa maki 33 zuwa 35.

Hukumar yanayin ta buƙaci alumma su riƙa shan ruwa sosai, sannan su kasance a wuri mai iska sosai tare da kaucewa wurare masu cinkoson alumma, kuma su rage zama ƙarƙashin rana.

Ta kuma shawarce su da su sanya hula da gilashi idan za su fita, kuma su sanya kaya marasa nauyi.

No comments