Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da bayar da kwangilar gina manyan ayyukan layin dogo guda uku a...
Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele ne ya sanar da hakan ga manema labarai a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da aka gudanar ranar Alhamis.
Ministan ya bayyana cewa an zabo waɗannan biranen ne saboda matsayin su na cibiyoyin kasuwanci da suka dogara da kansu, inda ya ce zuba jari a cikinsu zai haifar da sakamako mai kyau ga rayuwar talakawa.
Ayyukan da aka amince da su sun hada da:
Birnin Kano: Za a gina layin jirgin ƙasa na cikin gari (Kano Metro City Rail) wanda zai riƙa ɗaukar mutane zuwa sassan birnin.
Birnin Kaduna: Za a samar da tsarin jirgin ƙasa na "Light Rail" (wanda Gwamna Uba Sani ya nuna godiyar sa a kai a safiyar yau).
Birnin Legas: Za a fara aikin layin jirgin ƙasa na "Green Line" (Phase 1A).
Oyedele ya bayyana cewa waɗannan ayyuka guda uku za su ci kimanin dala biliyan 2.99 (kusan Naira tiriliyan hudu da rabi).
Ya ƙara da cewa za a samar da kuɗaɗen ne ta hanyar kamfanin hannun jari na Ma'aikatar Kudin Ƙasa (MOFI), tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin bayar da tallafi na musamman.
"Mun sani cewa babu ci gaba ba tare da ingantattun hanyoyi da sufuri ba. Waɗannan ayyukan an tsara su ne don bunƙasa kasuwanci, sauƙaƙa wa ma’aikata da ɗalibai zirga-zirga, da kuma kyautata rayuwar jama’a a waɗannan manyan biranen," in ji Ministan.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani bangare na shirin Shugaba Tinubu na tabbatar da cewa an farfaɗo da bangaren sufuri domin rage tsadar rayuwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a fadin ƙasar nan.
Masana tattalin arziki na ganin cewa idan aka kammala waɗannan ayyukan, birnin Kano da Kaduna za su zama manyan cibiyoyin sufuri a Arewacin Nijeriya, wanda hakan zai rage cinkoson ababen hawa da kuma saukaka jigilar kayan amfanin gona.

No comments