Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Himma Dai CBN: Tinubu Ya Sheƙa Wa Cardoso Ruwan Jinjina Da Yabo Kan Nasarorin Sauye-sauyen Tsarin Kuɗi Da Shirin Ƙara Jarin Bankuna

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, bisa gagarimar nasarar jagorantar sauye-sauyen da aka ...


Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, bisa gagarimar nasarar jagorantar sauye-sauyen da aka aiwatar, domin daidaita tsarin kuɗi da kuma dawo da amincewar masu zuba jari.

Tinubu ya yi wannan yabon ne yayin ƙaddamar da Filin Jirgin Sama na Gateway International Airport a Jihar Ogun.

Sannan kuma yabawa sauye-sauyen da CBN ya yi a kasuwar musayar kuɗaɗe ta waje, tsauraran matakan sa-ido da kuma shirin ƙara jarin bankuna.

“Ina so in yaba wa mutum guda a nan, Olayemi Cardoso, na gode sosai da duk abin da ka ke yi domin ƙasar nan,” inji Shugaban Ƙasar.

Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwar sa ga shugabancin CBN, inda ya bayyana Cardoso a matsayin mutum mai ladabi, maida hankali, kuma mai ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Kalaman Shugaban Ƙasar sun zo ne bayan wa’adin ranar 31 ga Maris da CBN ya sanya wa bankuna domin cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jarin banki da aka gabatar ƙarƙashin shirin ƙarfafa jarin bankuna.

Ana kallon wannan shiri a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan gyara da aka taɓa ɗauka a fannin bankuna a Nijeriya, inda aka ƙara mafi ƙarancin jarin bankuna zuwa naira biliyan 500 ga bankunan ƙasa da ƙasa, da kuma naira biliyan 200 ga bankunan ƙasa.

Ko da yake mafi yawan bankuna sun bi umarnin, har yanzu ana ci gaba da aikin ƙara jari ga Union Bank, Polaris Bank da Keystone Bank saboda wasu matsalolin doka da na tsare-tsare.

Sai dai CBN ya tabbatar wa masu ajiya da jama’a cewa bankunan da abin ya shafa suna da ƙarfi, suna aiki yadda ya kamata, kuma suna iya cika dukkan nauyin da ke kan su.

Matsalolin Union Bank sun biyo bayan binciken da CBN ya gudanar, wanda ya gano wasu manyan matsaloli a kundin bayanan kuɗin bankin.

Sakamakon binciken ya kai ga cire shugabannin bankin na Union da manyan jami’an gudanarwa a watan Janairun 2024.

A yanzu haka ana shari’a kan wannan mataki, inda CBN ke ƙalubalantar hukuncin kotu da ya nuna cewa cire shugabannin ba bisa ƙa’ida ba ne.

Haka kuma, Polaris Bank da Keystone Bank na ci gaba da shirin ƙara jari ƙarƙashin kulawar hukumomin sa-ido, bayan wasu matakan ceto da CBN ya ɗauka a baya.

A gefe guda kuma, ana ci gaba da kammala haɗewar Providus Bank da Unity Bank, yayin da ake jiran kammala wasu matakan doka da na tsari, waɗanda ake cewa sun kusa kammaluwa.
 

No comments