Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya miƙa godiyar sa da jinjina ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC),...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya miƙa godiyar sa da jinjina ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC), biyo bayan amincewa da manyan ayyukan raya kasa da kudinsu ya haura Naira tiriliyan ɗaya da biliyan 178 a jihar.
Cikin wata sanarwa da Gwamnan ya fitar don nuna jin daɗinsa, ya bayyana cewa waɗannan ayyuka za su sauya fasalin tattalin arziki da zamantakewar Jihar Kaduna baki ɗaya.
Babban aikin da ya fi ɗaukar hankali, kamar yadda Gwamnan ya bayyana, shi ne aikin samar da hanyar jirgin ƙasa na zamani a cikin birnin Kaduna (Light Rail). Wannan aiki zai tashi ne daga Rigachikun zuwa Sabon Tasha (kilomita 30), sannan wani layin ya tashi daga Millennium City zuwa Rigasa (kilomita 20).
Gwamnan ya bayyana cewa wannan aiki na kilomita 50, wanda darajar sa ta kai Naira tiriliyan daya, zai hadu da tsarin motocin bas-bas na zamani (BRT) da ake ginawa yanzu haka, domin saukaka zirga-zirga ga mazauna jihar.
"Kaduna ce jiha ta biyu a faɗin Nijeriya da za ta fara amfani da wannan tsarin jirgin ƙasa na Light Rail. Wannan ya nuna irin ƙwarin gwiwar da gwamnatin tarayya ke da shi a kan kyakkyawan shirin mu na sufuri," in ji Gwamna Uba Sani.
Baya ga aikin jirgin ƙasa, Gwamnan ya yaba da amincewa da aikin sake gina hanyar Mando zuwa Kaduna zuwa Birnin Gwari, mai nisan kilomita 122, wanda aka ware wa Naira biliyan 178.
Uba Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya taba ziyartar yankin Birnin Gwari kafin zaben 2023, inda ya ga halin rashin tsaro da lalacewar hanyoyi da mutanen yankin ke ciki, kuma ya yi alƙawarin kawo ɗauki.
Gwamnan ya ce: "Yau Shugaba Tinubu ya cika alƙawarin da ya ɗauka. Wannan hanya ba kawai sufuri za ta sauƙaƙa ba, za ta taimaka kwarai wajen karfafa tsaro, bunƙasa harkar noma, da kuma dawo wa mutanen yankin da ƙwarin gwiwa bayan shekaru na fargaba da killace."
Gwamnan ya tabbatar wa Shugaban Ƙasa cewa gwamnatin jihar za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an gudanar da waɗannan ayyuka cikin gaskiya da riƙon amana. Ya ƙara da cewa waɗannan ba ayyuka ne kawai ba, asali ne na gina makoma mai kyau ga jihar Kaduna.
A ƙarshe, ya sake jaddada godiyar ɗaukacin al'ummar Jihar Kaduna ga Shugaba Tinubu bisa wannan bajinta da ya yi na nuna adalci wajen raba ayyukan raya kasa a fadin ƙasar nan.

No comments