Daga Ashafa Murnai Barkiya Yayin da ake fama da gagarimar matsalar yawan maƙudan kuɗaɗen da bankuna suka bayar bashi, kuma biyan bashin ya...
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Yayin da ake fama da gagarimar matsalar yawan maƙudan kuɗaɗen da bankuna suka bayar bashi, kuma biyan bashin ya gagara, akwai masu ɗora laifin kan Babban Bankin Nijeriya (CBN), a matsayin sa na mai kula da kuma sa-ido kan dukkan bankunan Nijeriya.
To sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanayin yadda manya da ƙananan bankuna ke bayar da basussukan, to fa dole ne kacokan a ɗora laifin kan daraktocin bankunan da matsalar ta shafa da kuma manyan masu zuba jari a bankunan.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya bada umarni ga wasu bankuna cewa kada su raba ribar ƙarshen shekara-shekara, saboda ɗimbin bashin da bankunan suka bayar, wanda ba a biya ba, har ya riƙe wa bankunan wuya.
A irin wannan tsomomuwar bashin ne kamfanin ɗanyen mai da iskar gas, Nestoil mallakar Ernest Obiejesi ya ci bashin Naira Tiriliyan 2.9 a hannun wasu manya da ƙananan bankunan Nijeriya.
Masu Hannun Jari Ba ‘Yan Kallo Ba Ne:
A ƙarƙashin Dokar Kamfanoni da Harkokin Kasuwanci ta 2020 (CAMA 2020), masu hannun jari ba ‘yan kallo ba ne kawai, su ne ke da cikakken iko a harkokin shugabanci. Sashe na 238 ya bai wa taron gaba ɗaya iko, yayin da sashe na 271 zuwa 274 ke tanadin yadda ake naɗawa, cirewa da kuma biyan daraktoci.
Wannan yana nufin masu hannun jari ne ke zaɓar waɗanda za su tafiyar da banki, su kuma amince da albashin su da ladar su—wannan kuwa yana tasiri kai tsaye ga yadda suke gudanar da aiki.
Sashe na 238 ba kawai ƙa'ida ba ce, ginshiƙi ne na gaskiya da ɗaukar nauyi. Yana tabbatar da cewa masu kamfani ne ke zaɓar shugabanni, yana hana ƙungiyoyin daraktoci zama masu cin gashin kansu ba tare da kulawa ba. Haka kuma yana tabbatar da gaskiya a cikin tsarin naɗi, yana rage yiwuwar nadin ɓoye ko na son zuciya.
Wannan tsarin yana ƙarfafa ɗaukar alhaki, domin daraktoci sun san cewa masu hannun jari ne suka zaɓe su kuma za su iya cire su idan sun gaza.
Haka kuma yana taimaka wa masu kula (regulators) su san wane ne ke jagoranci da kuma yadda aka kai ga hakan.
A lokacin rikici, wannan sashe yana nuna cewa daraktoci ba su zo ne bisa kuskure ba—an zaɓe su ne da niyya, don haka dole a duba har da rawar masu hannun jari.
Amma a aikace, sau da yawa masu hannun jari kan goyi bayan faɗaɗa bayar da bashi domin samun riba mai yawa a lokacin bunƙasa tattalin arziki, sai kuma su koma baya su ɗora laifi kan wasu idan abubuwa suka lalace. Wannan hali yana haifar da matsala.
Daraktoci Sun Rigaya Sun Fuskanci Tsauraran Dokoki:
Ra’ayin cewa daraktoci ba su da alhaki a doka ba gaskiya ba ne. CAMA 2020 ya fayyace wajibai:
Sashe na 305 ya fayyace cewa: Wajibi ne daraktoci yu yi aiki cikin gaskiya don amfanin kamfani.
Sashe na 306: Su yi aiki da ƙwarewa da kulawa.
Sashe na 309: Su guji rikicin son-kai, son-rai da son-zuciya.
Haka kuma dokar bankuna ta BOFIA 2020 ta ƙara tsaurara wannan:
Sashe na 19 ya ce: Dole ne a bayar da bashi bisa ƙa’idojin banki masu kyau da fa'ida.
Sashe na 20: Ya hana bayar da bashi ga masu alaƙa da masu bayar da bashin, ba tare da bin ƙa’ida ba.
Idan aka karya waɗannan dokoki, akwai hukunci ciki har da tara, kora ko ma hukuncin kotu.
Saboda haka, tsarin doka ya riga ya tanadi yadda za a ɗauki mataki. Ba duk wani bashin da ya lalace ne sakamakon laifi ba—banki kasuwanci ne mai haɗari.
CBN Na Aiki Cikin Tsarin Da Doka Ta Gindaya:
Masu sukar CBN suna mantawa cewa Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗi, wato 'Banks and Other Financial Institutions Act' (BOFIA 2020), ta tanadi yadda za a ɗauki mataki a hankali:
Sashe na 33: Ya hana rabon riba da ƙari don kare jarin banki.
Sashe na 34: Ya bada damar cire daraktoci amma sai da hujja mai ƙarfi.
Wannan yana nuna cewa matakan suna zuwa ne a hankali:
Kariya kafin hukunci:
Dakatar da rabon ribar ƙarshen shekara-shekara da aka yi yanzu wata hanya ce ta kare tsarin banki, ba rauni ba ne. Wannan ya yi daidai da ƙa’idojin ƙasashe na duniya.
Shugabanci Tsari Ne Na Haɗin Gwiwa:
Shugabancin banki a yau ya haɗa da ɓangarori da dama:
Daraktoci, masu hannun jari, masu bin-diddigin lissafi, wato 'auditors', kwamitocin duba afkuwar matsala da tantance bashi.
Daraktoci masu zaman kan su suna taka muhimmiyar rawa wajen hana almubazzaranci.
Wasu Matsalolin da ke Haifar da Kasa Biyan Bashi ga Bankuna:
Rikicin bashin da ya faskara a biya, wato 'bad bebt', yana da alaƙa da:
Sauyin farashin kayayyaki, matsalar canjin kuɗi, raunin tsarin tattalin arziki da sauran su.
Idan manyan masu karɓar bashi sun gaza biya, tasirin yana shafar dukkan bankuna.
Buƙatar Tsari Mai Dorewa:
Masu hannun jari su riƙa taka rawar gani. Daraktoci su bi dokoki da ƙa’idoji. Tsarin bankuna ya ƙarfafa ɗabi’a mai kyau. CBN ta ci gaba da aiki cikin doka, kamar yadda a yanzu yake maida himma kan haka ɗin.
A ƙarshe, ɗora laifi kacokan kan CBN kawai ba daidai ba ne. Tsarin doka ya riga ya rarraba alhaki tsakanin:
Masu hannun jari, daraktoci, masu gudanarwa.
A duk inda aka samu laifi, to akwai hukuncin da doka ta tanada. Amma inda matsalar ta samo asali daga yanayin tattalin arziki, dole ne a ɗauki mataki cikin hikima.
Abin da ɓangaren banki ke buƙata ba zargin juna ba ne, sai dai tsarin gaskiya da ɗaukar alhaki daga kowane ɓangare—tun daga hukumar daraktocin banki, har zuwa masu hannun jari. Idan ba a yi haka ba, ko wane irin tsauraran matakan da aka ɗauka ba za su kawo canji mai ɗorewa ba.

No comments