Daga Aliyu Samba Fiye da shekaru goma, ɗaya daga cikin manyan ayyukan raya ƙasa na Nijeriya ya tsaya cik saboda kogi. Ba wai don rashin kuɗi...
Daga Aliyu Samba
Fiye da shekaru goma, ɗaya daga cikin manyan ayyukan raya ƙasa na Nijeriya ya tsaya cik saboda kogi.
Ba wai don rashin kuɗi ba, ko rashin kishin ƙasa, ko kuma ɗabi’ar nan ta jan ƙafar ma’aikatan gwamnati, duk da cewa waɗannan ma sun taka tasu rawar, a’a, Kogin Neja ne da kansa, da faɗinsa da zurfinsa, ya hana injiniyoyi sakat, ya cinye duk wani lokaci da aka ɗiba, ya kuma raba hanyoyin iskar gas din Nijeriya gida biyu.
To amma a ranar 30 ga watan Afirilun 2026, kwanaki uku kacal da suka gabata, wannan labari ya canza. Idan kai mai sayen dizal ne, ko mai biyan kuɗin wuta, ko kuma kana da wata sana’a a ƙasar nan, wannan labari naka ne.
Hukumar NNPC Limited ta sanar da kammala aikin ratsa Kogin Neja na bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3). Wannan bututu mai tsawon kilomita 130 an tsara shi ne don kwasar iskar gas har kafa (Standard Cubic Feet) biliyan 2 a kowace rana daga rafukan jihar Rivers zuwa garin Oben da ke jihar Edo.
Abin mamakin shi ne, ba ta sama aka ratsa kogin ba, kuma ba ta cikin sa ba; injiniyoyi sun hako rami ne mai nisan kilomita biyu a ƙarƙashin kasan kogin, ta amfani da fasahar Horizontal Directional Drilling, irin wadda aka yi amfani da ita wajen gina ramukan ƙasa da suka haɗa Ingila da Faransa. Wannan shi ne babban aikin injiniya mafi sarkakiya da aka taba yi a gida Nijeriya, kuma kamfanin ƙasar nan mai suna PCE Nig. Limited ne ya aiwatar da shi.
An fara wannan aiki ne tun a shekarar 2016, inda aka sa ran kammala shi a watan Maris din 2024. Lokacin ya wuce, aka sake sa watan Agusta 2024 shi ma ya wuce. Har zuwa watan Agustan 2025, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas) yana cewa aikin "ya kusa kammala."
Dalilin jinkirin shi ne Kogin Neja. Yanayin yankin Neja Delta yana da matuƙar wahalar gudanar da manyan ayyukan injiniya saboda ƙasa mai laushi, ruwan ƙarƙashin ƙasa mai yawa, da kuma kasan kogin da ya ƙi yarda da duk wani tsarin hako rami na al'ada. Duk lokacin da injiniyoyi suka gwada, sai wata matsalar ta fito. Sai da aka kwashe shekaru biyu ana canza fasali da dabarun aiki don kawai a tabbatar an yi aiki mai inganci a ƙarƙashin wannan kogi mai sauyawa.
Abin farin ciki shi ne yadda Nijeriya ta yi amfani da gogewar da ta samu a baya. A watan Yunin 2025, NNPC ta kammala wani aikin ratsa Kogin Neja na bututun AKK (Ajaokuta-Kaduna-Kano) a bangaren Arewa. Waɗancan injiniyoyin sun fara warware matsalar kogin a can. Shugaban kamfanin NNPC na kasa, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa aikin OB3 ya samu nasara ne ta hanyar amfani da darussan da aka koya daga aikin AKK. Wannan babban ci gaba ne; Nijeriya, a karon farko, ta yi koyi da kanta.
Me Wannan Ke Nufi Ga Talaka?
Don fahimtar mahimmancin wannan, kwatanta tsarin iskar gas din Najeriya da jikin dan adam. Yankin Neja Delta shi ne zuciya, bututun kuma su ne hanyoyin jini. Shekaru da dama, bututun OB3 ya kasance a matsayin hanyar jini da ta yanke a tsakiya. Iskar gas din da ya kamata ya kunna masana'antu a Legas, ya haska gidaje a Abuja, ya kuma raya masana'antu a Kano, sai dai a kone shi a sararin samaniya ko kuma ya tsaya a ƙarƙashin ƙasa.
Yanzu da wannan aiki ya kammala, za a samu karin kafa miliyan 500 na iskar gas a kasuwar gida. Ma'anar wannan ga talaka ita ce: za a samu ƙarin wutar lantarki a gidaje, sannan za a rage dogaro da janareta mai cin dizal wanda ya zama tamkar wani haraji ga 'yan ƙasa.
Attajiri Aliko Dangote ya taba faɗin cewa kammala aikin OB3 zai janyo sabon jarin da ya kai dala biliyan biyu ($2bn) ga tattalin arzikin Nijeriya. Wannan ba maganar gwamnati ba ce; magana ce ta dan kasuwa mai hangen nesa. Masana'antun takin zamani, siminti, da sarrafa abinci duk suna jiran wannan iskar gas don faɗaɗa ayyukan su.
Haka kuma, bututun OB3 da AKK yanzu sun zama tsari daya cikakke. OB3 zai dauko gas daga Kudu ya kai shi Yamma, yayin da AKK zai dauke shi ya kai shi Kaduna da Kano. Ba tare da OB3 ba, bututun AKK zai kasance kamar babbar hanyar mota ce da ba ta da mahadar shiga.
Dole mu jinjinawa kamfanin PCE Nig. Limited. A kasar da aka saba ba da manyan ayyuka ga baki, kamfanin Nijeriya ne ya hako rami kilomita biyu a ƙarƙashin ɗaya daga cikin manyan ƙoramun Afirka. Wannan ya nuna cewa injiniyoyin mu sun kai matsayin da za su iya warware duk wata matsala.
Sannan kuma dole mu yi jinjina ga gwamnatin Shugaba Tinubu. Ta yi alƙawarin "Sabunta Fata" (Renewed Hope), kuma sannu a hankali, tana cika wannan alƙawari ta hanyar kammala ayyuka daya bayan daya. Abin da ya rage yanzu shi ne talakawa su fara ganin iskar gas din ya fara gudu a cikin bututun.
Nijeriya ta sa gaba cewa nan da shekarar 2030 za ta rika samar da gangar mai miliyan 3 da kafa biliyan 12 na iskar gas a kowace rana. Aikin OB3 wani babban mataki ne na tabbatar da cewa kasar nan ba za ta sake bari yanayin ƙasa ya dakatar da ci gaban ta ba.
Allah Ya taimaki Nijeriya. Ameen

No comments