Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Buƙaci Gwamna Sule Ya Dawo Da Ƙarin Albashi Na Shekara-shekara Ga Ma’aikata

Daga Zubairu Lawal, Lafia Ƙungiyoyin ƙwadago a Jihar Nasarawa sun roƙi Gwamna Abdullahi Sule da ya dawo da tsarin ƙarin albashi na shekara-s...

Daga Zubairu Lawal, Lafia

Ƙungiyoyin ƙwadago a Jihar Nasarawa sun roƙi Gwamna Abdullahi Sule da ya dawo da tsarin ƙarin albashi na shekara-shekara ga ma’aikatan jihar.

Ƙungiyoyin ƙwadagon, waɗanda suka haɗa da Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC), sun yi wannan kira ne a ranar Juma’a a Lafia yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2026.

Shugaban NLC, Kwamared Ismaila Okoh, ya ce wannan roƙo ya zama dole domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar kiyaye matsayinsu na girma a aikin gwamnati, wanda ya ragu.

Ya bayyana cewa ma’aikata sun sha wahala sakamakon rashin samun ƙarin mataki (step increment) a kowace shekara, yana mai cewa wannan ya saba wa tsarin aikin gwamnati.

Ya kuma roƙi a aiwatar da ƙarin Naira 20,000 a fanshon kowane wata ga masu ritaya na jihar, tare da ƙara la’akari da ƙarin albashi ga masu ritaya a matakin ƙananan hukumomi.

Har ila yau, ya buƙaci a samar da isasshen kuɗi ga Hukumar Fansho domin ta iya biyan kuɗin gratuti (haƙƙin ritaya) daga inda aka tsaya a yanzu.

Ya ƙara da cewa: “Mun amince da ƙoƙarin gwamnanmu wajen tabbatar da cewa duk masu ritaya sun samu haƙƙinsu, kuma ya zuwa yanzu an biya har zuwa waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2013.”

Sai dai ya yaba da aiwatar da mafi ƙarancin albashi, tare da roƙon a hanzarta kammala tsarin aiwatar da ƙarin kashi 25 da 35 na CONHESS ga ma’aikatan lafiya, la’akari da yawan aikin da suke yi.

Ya ce: “Wannan ya zama dole musamman duba da cire tallafin mai, wanda ya jefa ma’aikata cikin wahala, har ya sa mafi ƙarancin albashi na N70,000 ya zama ba shi da tasiri.”

Ya kuma yi kira ga ma’aikata su ƙara ƙoƙari domin su nuna cewa sun cancanci irin jarin da gwamnati ke zuba a kansu.

A nasa bangaren, Shugaban TUC, Kwamared Isa Yusuf, ya bayyana gwamnan a matsayin mai kula da jin daɗin ma’aikata, wanda ke ba da muhimmanci ga walwalarsu.

Ya ce aiwatar da ƙarin fansho zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar masu ritaya.

Ya kuma roƙi gwamnan ya kafa wata sashen da zai riƙa wallafa biyan gratuti na kowane wata domin tabbatar da ana bin tsarin biyan masu ritaya bisa wanda ya fara yin ritaya.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya yi ayyuka da dama wajen inganta jin daɗin ma’aikata da kuma rage gibin ababen more rayuwa a jihar.

Ya lissafa wasu daga cikin ayyukan gwamnan da suka haɗa da gadar sama (flyover) da hanyar karkashin ƙasa (underpass) a Lafia, ayyukan irin waɗannan a Akwanga, Keffi da Karu, ginin babban sakatariyar jihar, tashoshin mota a Lafia da Karu da sauransu.

Sauran sun haɗa da hanyar kewaye a Akwanga, amincewa da bai wa ma’aikatan gwamnati gidaje na mallaka (owner-occupier), da kuma ba wa ma’aikatan wucin gadi aikin dindindin.

Saboda haka, ya tabbatar wa gwamnati cikakken goyon baya da jajircewa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryenta domin cigaban jihar gaba ɗaya.

A saƙonsa, Gwamna Sule, wanda Barrista Abigail Waya, Shugabar Ma’aikatan Gwamnati ta wakilta, ya gode wa ƙungiyoyin ƙwadago da ma’aikata bisa goyon bayan da suka ba gwamnatinsa tun daga 2019.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da manufofi da shirye-shirye da dama domin inganta yanayin aiki da rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa ya ɗauki sama da ma’aikata 8,000 a makarantu na sakandare da manyan makarantu, sama da 2,000 a fannin lafiya, sannan ya ba wa fiye da 1,000 ma’aikatan wucin gadi aiki na dindindin, tare da ci gaba da ƙoƙarin ɗaukar ƙarin malamai.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa sauran wa’adinsa zai mayar da hankali wajen sauya fasalin jihar gaba ɗaya da inganta jin daɗin al’ummarta.

Da yake zantawa da manema labarai Sakataren Kungiyar NURTW reshen Jihar Nasarawa Alhaji Adamu Idiris Abdullahi ya shawarci Gwamnati da ta kara fadada tashohin mota a sabobin hanyoyin da aka kirkira na by-pas saboda gaba.

Ya Kuma shawarci Gwamnati da ta ɗaga ƙananan tashohin mota da ke cikin gari su koma Babban garejin Yahaya Sabo, saboda rage cin koso a cikin gari. Da tabbatar da tsaron lafiyan al'umman Jihar.

Ya Kuma roƙi Gwamnatin Jihar da ta tallafa wa ƙungiyar NURTW da tsarin motochin sufuri, Ko da ba shi ne. Saboda wasu za su iya mallakar matochi nasu na kansu. Kuma Gwamnatin za ta ƙara samun kuɗaɗen shiga

 

No comments