Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

HUKUNCIN KOTUN KOLI: Mun Yi Nasarar Hana Wike Mallake PDP – Gwamna Bala

  * Zuciyar Mu Ta PDP Ce, Amma Dole Mu Fita Don Yin Takara, Zan Nemi Sanata  Daga Khalid Idris Doya  Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya...

 
* Zuciyar Mu Ta PDP Ce, Amma Dole Mu Fita Don Yin Takara, Zan Nemi Sanata 

Daga Khalid Idris Doya 

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bayyana cewar bayan hukuncin da kotun koli ta yanke kan rikicin jam'iyyar PDP, a halin yanzu dukkanin ɓangarorin da ke rigima da ta ɓangarensa wacce Barr. Tanimu Turaki ke jagoranta da na ministan Abuja Nyesom Wike duk ba wacce ta samu abun da take nema.

Gwamnan, sai dai ya gode wa Allah da cewa ƙoƙarinsu ya kai ga hana Wike samun damar mallake jam'iyyar adawa ta PDP shi kaɗai.

A kan hakan, gwamnan jihar Bauchi, ya sanar da cewa a kowani lokaci daga yanzu za su fice daga PDP zuwa wata jam'iyya ta daban domin bai wa magoya bayansu da ke da niyyar yin takara a zaɓen 2027 damar shiga a fafata da su zaɓukan da ke tafe.

Gwamnan ya sanar da cewa bisa ƙiranye-ƙiranyen da yake ta samu daga wajen al'umma ya amince zai tsaya takarar Sanatan Bauchi ta Kudu a zaɓen 2027 da ke tafe a wata wata jam'iyya ba PDP ba.

Bala Muhammad wanda ya shaida hakan a hirarsa da BBC Hausa da suka wallafa a ranar Asabar dangane da hukuncin kotun koli kan rikicin cikin gida na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, inda ya nuna takaici kan shirin gwamanti mai mulki na neman hana 'yan adawa damar shiga zaɓen da ke tafe ta wajen yin amfani dabarbaru.

"A matsayinmu na 'yan demukuraɗɗiya kuma na PDP wanda muke da tarbiyya na biyayya kuma muke ganin kimar waɗanda suke da hurumi na shari'a, mun ɗauki hukuncin yadda ya zo bisa ƙaddara saboda abun kamar ba za a ce mun faɗi warwas ba ko a ce ɗaya gefen sun yi nasara ba.

"Kowa ya san dai yadda muka jajirce muka kai har zuwa wannan matakin, muka kai kwaloluwa wajen bin haƙƙin al'umma, musamman masoya jam'iyyar PDP da masoyan demuraɗiyya a Nijeriya. Shi ya sa wannan matsayin a wajen mu ba za mu ce mun faɗi har ƙasa ba; amma kuma kodayake su ma sun faɗi, mu ma ba mu samu abun da muke so ba, tun da taron da muka yi a Ibadan ba a yarda da ita ba, su kuma abun da suka kafa da suka ce sune shugabanni su ma ba a yarda da su ba."

Da ya ke bayani kan halin da PDP ta samu kanta a ciki a halin yanzu, ya ce bisa dokar jam'iyyar yanzu dattawan jam'iyyar ke rike da shugabancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a kafa kwamitin riƙon ƙwarya.

"Dattaɓai wato BoT na jam'iyya kamar yadda kundin tsarin mulkinmu ya tanada za su ɗauki ragamar shugabancin wannan jam'iyyar har zuwa lokacin da za a sanya shugabannin riƙon kwarya tun da Shari'a ba ta yarda da waɗanda suke ciki ba," ya faɗi.

Gwamnan ya kuma zargi da ministan Abuja Nyesom Wike da cewa shi ɗan APC ne a ɓoye da ya yi aikin ruguza PDP, "Ai mu ne yanzu muke alaƙaƙai tun da shi Wike ai a APC ya ke shi da 'ya'yansa da magoya bayansa duk a APC suke."

Da aka tambaye shi kan cewa duk da Wike bai bayyana cewa ya koma APC ba? Sai gwamnan ya amsa da cewa, "Ai kun ga ɗansa zai tsaya a matsayin ɗan takarar majalisar tarayya da kuma wasu hadimansa duk sun koma APC; Ai shi (Wike) daman ya zama mana dagwalo ne a cikin jam'iyyar PDP kuma ya cimma burinsa; amma muma mun cimma burinmu tun da ba mu bar masa jam'iyyar ta zama tasa ba. 

"Sai dai kuma dole muna da buƙatar mu bada wani mataki ko matakala wa magoya bayanmu su shiga wasu jam'iyyu saboda su samu a zaɓesu a kujerun da suke so."

Gwamnan ya ce sun riga sun tattauna da jam'iyyu da suke ganin za su gaya wa magoya bayansu su shiga domin samun damar yin takara a zaɓen 2027.

"Tun da babu lokaci da za a ce har a sa wato shugabancin riƙon kwarya har INEC ta yarda da ita a cikin kwana 5 ko 6. To, dole ne mu yi amfani da hikima da dabarbaru mu samu wata jam'iyya da suke da tsafta wacce ba ta matsala mu sa mutanenmu domin su samu su tsaya takarar zaɓukan da suke tunkarowa a 2027".

Ya yi zargin halin da ake ciki a Nijeriya da yunƙurin hana 'yan adawa shiga zaɓe.

"A yadda suka tsara kamar abu ne wato ne na Yahudanci aka yi yadda zai hana mutane dama su tsaya zaɓe, su a barsu su kaɗai su yi zaɓe. Shi ya sa dole ne mu yi hikima mu shiga waɗansu jam'iyyu kodayake zuciyarmu ta PDP ne amma ba yadda muka iya. Abun da ya rage kwana biyar ne a cikin kwana biyar cikin hukuncin Allah mun riga mun tantance inda za mu sanya mutanmu su ci gaba."

Ya ƙara da cewa duk da su za su fita a PDP amma asalin jagororin jam'iyyar za su cigaba da fafata neman haƙƙin jam'iyyar, "Amma su asalin shugabannin PDP za su zauna su ci gaba da faɗa da yake gabansu wato su Tanimu Turaki tun da ya zama musu haƙƙi su kwato mana 'yancinmu; mu kuma da muke son mu tsaya a wasu wurare za su bai wa mutane dama domin su yi takara.".

Ya ce nan kusa za a fara jin inda magoya bayansu a jihohi za su koma domin samun damar yin takara. Ya nemi magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu inda ya sha alwashin cewa za su yi duk mai yiyuwa wajen kwato jam'iyyar PDP.

Wakilinmu ya labarto cewa a halin yanzu ana ta raɗe-raɗin cewa gwamnan da magoya bayansa a jihar Bauchi za su shiga jam'iyyar APM domin neman damar yin takara a zaɓen 2027.
 

No comments