Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farashin Ɗanyan Mai Ya Faɗi A Kasuwannin Duniya

Farashin ɗanyan mai ya faɗi, yayin da hannayen jari a kasuwannin duniya suka tashi bayan rahotannin da ke cewa Amurka da Iran na gab da cimm...




Farashin ɗanyan mai ya faɗi, yayin da hannayen jari a kasuwannin duniya suka tashi bayan rahotannin da ke cewa Amurka da Iran na gab da cimma kawo ƙarshen yaƙin.

Farashin mai nau'in Brent ya faɗi zuwa ƙasa da dala 100 duk ganga.

Farashin ɗanyan man na ta hawa da tashi tun soma yaƙin AMurka da Isra'ila kan Iran, bayan da Amurka da Iran suka taƙaita zirga zirga ta Mashigar Hormuz.

A gefe guda kuma, kamfanonin jiragen sama sun rage tashin jirage 13,000 a faɗin duniya cikin watannan, a yayin da farashin man jirgin ke ta hauhawa.

Masu sharhi sun ce lamarin ya shafi kusan fasinjoji miliyan biyu.

No comments