Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Wa Masu Digirin Girmamawa Kiran Kansu “Dr”

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabuwar doka wadda ta hana duk wanda aka ba digirin girmamawa (Honorary Degree) amfani da laƙabin “D...




Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabuwar doka wadda ta hana duk wanda aka ba digirin girmamawa (Honorary Degree) amfani da laƙabin “Dakta” a gaban sunansa a kowane fanni na hukuma, ilimi ko sana’a, tana mai cewa hakan na nuni da yaudara da karkatar da gaskiyar cancantar ilimi.

Ministan Ilimi, Malam Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja yayin ganawa da ’yan jarida, inda ya ce an amince da sabuwar manufar ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) domin daidaita tsarin bayar da digirin girmamawa a jami’o’in Nijeriya.

A cewarsa, mataimakiyar ministan ilimi, Suwaiba Ahmad, ta kasance tare da shi yayin bayyana matakin da ya ce zai kawo ƙarshen cin zarafin wannan tsarin ilimi da aka dade ana yi.

Ministan ya bayyana cewa gwamnati ta gano yadda ake amfani da digirin girmamawa wajen siyasa, neman tagomashi da kuma tara kuɗi, maimakon karrama cancanta da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

Ya ce: “Abin da muka fara gani shi ne yadda ake amfani da digirin girmamawa wajen siyasa da neman ribar kuɗi, har ma ana ba wasu manyan jami’an gwamnati yayin da hakan bai dace da ƙa’idojin bayar da irin wannan karramawa ba.”

Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wanda aka ba digirin girmamawa ba zai ƙara saka “Dr” a gaban sunansa ba, sai dai ya rubuta shi a bayan suna tare da bayyana cewa digirin girmamawa ne.

Ministan ya bayar da misali da cewa za a rubuta kamar haka: “Alhaji Musa Bello, D.Lit (Doctor of Literature, Honoris Causa)” ko “Hajiya Aisha Umar, LL.D. (Honoris Causa)”.

Ya ce wannan tsari zai bambanta digirin ilimi na gaskiya da na girmamawa, domin kare martabar ilimi a ƙasar.

Alausa ya ƙara da cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin amfani da digirin girmamawa a matsayin na karatu na gaskiya, yanzu za a ɗauki hakan a matsayin laifin ilimi da zai iya jawo hukunci.

Sabuwar manufar ta kuma takaita nau’o’in digirin girmamawa da jami’o’i za su iya bayarwa zuwa huɗu kacal, wato Doctor of Laws (LL.D), Doctor of Letters (D.Lit), Doctor of Science (D.Sc), da Doctor of Humanities (D.Arts).

Haka kuma, an haramta wa jami’o’in da ba su kai matakin bayar da digiri na uku (PhD) ba su riƙa bayar da digirin girmamawa.

Gwamnati ta kuma bayyana cewa duk takardun digirin girmamawa dole ne su nuna a fili kalmar “Honorary” ko “Honoris Causa”.

Ministan ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) za su fitar da umarni ga dukkan shugabannin jami’o’i domin tabbatar da bin wannan doka.

Haka kuma, gwamnati za ta fara sa ido kan tarukan karramawa tare da haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai domin dakile amfani da lakabi ba bisa ƙa’ida ba.

No comments