Daga Hussaini Yero, Gusau Ɗan takarar Sanata a jam'iyyar APC na shiyyar Zamfara ta Arewa, Dr Sani Abdullahi Shinkafi, ya karbi dubban ma...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Ɗan takarar Sanata a jam'iyyar APC na shiyyar Zamfara ta Arewa, Dr Sani Abdullahi Shinkafi, ya karbi dubban magoya bayan abokan hamayyar sa da kuma amsa kiran su na Tsayawa takara Sanata na Jamiyyar APC A Zamfara Ta Arewa,a gidan sa da ke Gusau.
Dr Abdullahi Shinkafi wanda ya karbi magoya bayan abokan hamayyar sa da suka sauya mubaya’a zuwa bangarensa, ya ce ya yanke shawarar siyan Fam na takarar Sanata ta shiyyar ne saboda kiraye-kiraye da dama daga al’ummar shiyyar da ma wajen shiyyar, domin ya ƙarfafa dangantakar abokantaka da ke akwai tsakanin sa da mazabar sa.
Ya ci gaba da cewa shiyyar ta sha wahala matuƙa na watsi daga wakilan shiyyar na baya musamman kan batun rashin tsaro wanda ya yi mummunar illa ga shiyyar ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.
Dr Abdullahi Shinkafi ya ce idan suka zabe shi a Majalisar Dattawa, zai yi duk abin da ya dace don kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankunan da ma Zamfara baki daya.
Ya ce zai hada kai da takwarorinsa a majalisar domin gabatar da kudirori da dama da za su jawo hankalin Gwamnatin Tarayya a fannoni da dama na ci gaba zuwa shiyyar sanatan Zamfara ta Arewa musamman kan batutuwan rashin tsaro da sauran ci gaba masu ma’ana.
Da yake magana a madadin ƙungiyar, Hon. Abdullahi Zurmi ya ce sun yanke shawarar sauya mubaya’ar su zuwa ga Dr Sani Abdullahi Shinkafi ne saboda ƙwarin gwiwar da suke da shi a kansa.
Ya ce Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya tabbatar da kansa a matsayin mai himma, mai kishin jin dadin al’umma kuma mai damuwa da ci gaban al’umma gaba daya.
Ya yi alkawarin ba da cikakken goyon bayansu ga Dr Sani Abdullahi Shinkafi a gwagwarmayar wakiltar mazabar Sanata Zamfara ta Arewa a Majalisar Dattawa da ke Abuja ta hanyar fara gagarumin gangami na wayar da kan jama’a kan amfanin wakiltar Dr Sani Abdullahi Shinkafi ga shiyyar.
Hon.Ya bayyana kwarin gwiwar sa cewa wakiltar Dr Sani Shinkafi zai kare muradun da burin al’ummar Arewa Maso Yamma.
Hon Abdullahi Zurmi ya ce da yawa daga cikin wakilan da suka gabata sun gaza cika alƙawari.

No comments