Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Jigilar Maniyyata 50,000 Na Aikin Hajjin 2026 A Abuja

● Ku Kasance Masu Kyawun Hali Don Kare Kimar Nijeriya — Shettima Daga Aliyu Samba ​Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi k...


● Ku Kasance Masu Kyawun Hali Don Kare Kimar Nijeriya — Shettima

Daga Aliyu Samba

​Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su kiyaye ɗabi’u nagari waɗanda za su fito da martabar Nijeriya fili, sannan su kasance jakadu nagari ga ƙasar su yayin gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki.

​Shettima ya bayyana maniyyata a matsayin wakilan Nijeriya a idon duniya, inda ya buƙace su da su nuna kyakkyawar ɗabi’a ta hanyar bin dokoki da oda na ƙasar Saudiyya.

​Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da ya ke ƙaddamar da jigilar maniyyata ta farko na shekarar 2026 a Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Ya nanata cewa gwamnati ta jajirce wajen tabbatar da tsaro, tsari, da jin dadin dukkan mahajjata.

​“Ku jakadun Nijeriya ne. Kuna ɗauke da hoton ƙasar mu da mutuncin al’ummar mu. Halayen ku su nuna tarbiya, tawali’u, haƙuri, da gaskiya,” in ji shi.

​An fara jigilar ne da mahajjata kusan 500 daga Jihar Kogi zuwa ƙasar Saudiyya, yayin da jimillar maniyyata 50,000 ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin na bana daga Nijeriya.

​Da yake jawabi a wurin taron, Shettima ya bayyana cewa aikin Hajji wata tabbatacciyar yarjejeniya ce tsakanin gwamnatin Nijeriya da ’yan kasa, inda ya ce ya zama wajibi kan gwamnati ta sauke nauyin kula da su, su kuma maniyyata su kare mutuncin kasar.

​Ya kara da cewa: “Aikinmu ne mu tabbatar kowane maniyyaci ya yi wannan tafiya ba tare da wata wahala ko fargaba ba. Nasarar wannan aikin ba ta dogara ne kawai kan yawan jiragen da suka tashi ba, a’a, tana ga jin daɗin mahajjatanmu da kuma kauce wa duk wata nakasu da za a iya kauce mata.”

​A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana aikin Hajji a matsayin wata dama ta musamman da ke buƙatar sadaukarwa ga Allah. Ya buƙaci maniyyata da su ci gaba da addu’o’i ga Nijeriya, musamman kan zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

​Haka zalika, ya nemi a taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Shettima da addu’a yayin da suke ƙoƙarin gyara ƙasar nan ta hanyar manufofin su na "Sabunta Fata" (Renewed Hope).

​Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Ƙasa (NAHCON), Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa hukumar tana nan kan bakarta na tabbatar da jin daɗin ’yan Nijeriya. Ya bayyana cewa hukumar tana fuskantar garambawul ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu don tabbatar da gaskiya da kuma sauya fasalin aikin Hajji a ƙasar.

​Taron ya samu halartar Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, da wakilin Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, waɗanda duka suka jaddada ƙudurin gwamnati na ganin an kwashe mahajjata lafiya an kuma dawo da su lafiya.

No comments