Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hon. NaLaraba Ya Sauka Daga Takarar Gwamna,Ya Koma Sanatan Nasarawa Ta Kudu

Daga Zubairu Lawal, Lafia Ɗan majalisar wakilai na tarayya da ke wakilyar Nasarawa ta Kudu a jihar Nasarawa, Honorabul Abubakar Hassan Nalar...


Daga Zubairu Lawal, Lafia

Ɗan majalisar wakilai na tarayya da ke wakilyar Nasarawa ta Kudu a jihar Nasarawa, Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya sanar da janyewar sa daga takarar kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa a ƙarƙashin jam'iyyar APC, inda ya ce a yanzu ya koma neman kujerar Sanata don wakiltar mazaɓar a majalisar dattawa ta Kudancin jihar.

Ya sanar da haka ne a lokacin wata ganawa ta musamman da mambobin ƙungiyar yaƙin neman takarar sa ta kujerar gwamna daga Ƙananan Hukumomi 13 na jihar.

A cewar Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya yanke shawarar yin haka ne a matsayin sa na mai kishin ƙasa da ke saka ci gaban jihar a gaba a kullum, da kuma yin biyayya da girmama matakin Gwamnan jihar mai ci yanzu, Injiniya Abdullahi Sule na zaɓin Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda zai gaje shi a kujerar gwamnan a zaɓen 2027.

Sannan ya ce, kasancewar sa cikakken ɗan jami’iyyar APC, kuma ya riga ya yi alƙawari cewa a ƙarshe duk wanda Gwamna Sule ya zaɓa cikin su ‘yan takarar zai mara masa baya, ba wai don ya karaya ko ya gaza ba.

Ɗan takarar ya kuma yi amfani da damar inda ya umurci ɗimbin magoya bayan sa daga duka Ƙananan Hukumomin jihar 13 su mara wa zaɓin Gwamnan, wato Sanata Ahmed Aliyu Wadada baya a zaɓen don ɗorawa daga inda Abdullahi Sule zai tsaya.

Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa daga bisani ɗan takarar gwamnan, wanda ya koma neman Sanatan, Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya kuma gana da manema labarai inda ya tabbatar musu da matakin nasa na canja takarar a hukumance.

Bayan ya bayyana Masu Irin ayyukan alheri da ya yi wa mazaber Doma, Kena da Awe. Da yadda ya taimaka wa mata da Matasa .

Daga nan sai ya bayyana wasu daga cikin kyawawan shirye-shirye da tsare-tsaren ayyukan ci gaba da zai gudanar don amfanin al’ummar sa na mazaɓar Sanatan idan Allah ya ba shi nasara.

Daga bisani ɗan takarar ya kuma jagoranci ɗimbin magoya bayan nasa zuwa ofishin jami’ar APC na jihar da ke nan Lafiya, inda ya sayi fom na nuna sha’awar neman takarar Sanatan.
 

No comments