Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Asabar domin rangadin ƙasashe uku—Faransa, Kenya da Ruwanda. Wannan bayani ya fito n...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Asabar domin rangadin ƙasashe uku—Faransa, Kenya da Ruwanda.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mista Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare.
Da yake fayyace yadda tafiyar za ta kasance, Onanuga ya ce matakin farko na tafiyar Shugaba Ƙasar zai kasance a ƙasar Faransa, daga nan kuma zai tafi Nairobi ta ƙasar Kenya domin halartar taron "Africa-France Summit" wanda aka tsara zai fara a mako mai zuwa.
Taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto suke jagoranta tare, zai maida hankali kan sauyin makamashi, bunƙasa masana’antu marasa aiki da fetur, sauyin dijital, sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya, da kuma matakan yaƙi da sauyin yanayi.
Onanuga ya ce halartar Shugaba Tinubu a taron daga ranar 11 zuwa 12 ga Mayu zai ƙara jaddada ƙudirin Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwar dabaru da ƙasashen Afrika da Jamhuriyar Faransa.
Taron mai taken “Africa Forward: Africa-France Partnerships for Innovation and Growth”, zai samar da babban dandali ga shugabannin Afrika da takwarorin su na Faransa domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar, ciki har da sauyin tattalin arziki, jure wa sauyin yanayi, bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa, cigaban fasaha, da kuma gina zaman lafiya.
Bayan kammala taron na Kenya, Tinubu zai tafi Kigali, babban birnin ƙasar Ruwanda, domin halartar taron shekara-shekara na "Africa CEO Forum" wanda za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu.
Taron na bana mai taken “Scale or Fail” shi ne mafi girman taron shugabannin kamfanoni masu zaman kan su na Afrika, masu zuba jari, da masu tsara manufofi, inda za a mai da hankali kan hanzarta sauyin tattalin arziki ta hanyar haɗin kai, haɗa yankuna, da ƙara zuba jari tsakanin ƙasashe.
Ana gudanar da taron ne tare da haɗin gwiwar "International Finance Corporation", kuma zai haɗa sama da manyan shugabanni 2,000 da jagororin ƙasashe domin tattauna dabarun gina masana’antu masu ƙarfi da gasa.
A dukkanin tarukan biyu, Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabai da za su nuna gyare-gyaren da gwamnatin sa take yi domin mayar da Nijeriya cibiyar da ta dace don zuba jari da bunƙasa tattalin arziki.
Haka kuma, zai yi ganawa da manyan shugabannin kasuwanci na duniya da na Afrika.
Shugaban zai tafi tare da wasu ministoci da manyan mataimakan sa, kuma ana sa ran zai dawo Nijeriya bayan kammala taron Ruwanda.

No comments