A yau, al’ummarmu na fuskantar wani babban ƙalubale da ke ci gaba da yaɗuwa cikin sauri musamman a tsakanin matasa, wato matsalar ɗaukar da ...
A yau, al’ummarmu na fuskantar wani babban ƙalubale da ke ci gaba da yaɗuwa cikin sauri musamman a tsakanin matasa, wato matsalar ɗaukar da kuma yaɗa bidiyon tsiraici ta kafafen sada zumunta. Wannan mummunar ɗabi’a ta zama tamkar wata cuta da ke cinye tarbiyya, mutunci da kuma kyawawan ɗabi’un Hausawa da Musulunci ya gina tun shekaru masu yawa.
Abin takaici ne yadda ake yawan samun rahotannin wasu ’yan mata da samari suna shiga soyayya ba tare da iyaka ko tsoron Allah ba, har su kai ga ɗaukar hotuna ko bidiyoyi yayin aikata fasiƙanci. A wasu lokutan budurwar ce da kanta ke tura wa saurayi irin waɗannan bidiyoyi saboda tsananin yarda ko soyayya, yayin da a wasu lokutan kuma saurayin ne ke ɗaukar bidiyon ba tare da cikakken sanin budurwar ba. Daga baya idan rikici ya shiga tsakaninsu, ko kuma saboda son ɗaukar fansa, sai a ga an yaɗa bidiyon a WhatsApp, Facebook, TikTok da sauran kafafen sada zumunta.
Kwanakin baya, kafafen sada zumunta sun cika da labarin wata yarinya da bidiyonta ya bazu a intanet bayan an ce saurayinta ne ya yaɗa shi. Cikin sa’o’i kaɗan, dubban mutane sun sauke bidiyon, wasu suna tura wa juna, wasu suna yin sharhi da izgili, yayin da iyalanta ke cikin matsanancin tashin hankali da kunya. Wannan lamari ya sake nuna yadda rashin tsoron Allah da rashin kiyaye sirri ke lalata rayuwar mutane cikin lokaci kaɗan.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu matasa ke kallon wannan a matsayin “wayewa” ko “romance”, alhali kuwa babban bala’i ne ga mutum da al’umma baki ɗaya. Addinin Musulunci ya hana zina, ya kuma hana duk wani abu da zai kai zuwa gare ta. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce kada ma a kusanci zina domin ita mummunar hanya ce. Saboda haka, ɗaukar bidiyon tsiraici ko hotunan batsa wani babban laifi ne da ke jefa mutum cikin fushin Allah.
A yau da yawa daga cikin waɗannan bidiyoyi da ake yaɗawa sun zama sanadin lalacewar rayuwar wasu ’yan mata har abada. Akwai waɗanda suka rasa damar aure saboda wani tsohon bidiyo da ya bayyana a intanet. Wasu sun shiga damuwa da matsanancin tashin hankali har ta kai ga suna ƙaurace wa jama’a saboda kunya. Wasu ma sun faɗa cikin matsalar tabin hankali sakamakon zagi da tozarci daga al’umma.
Haka kuma, yaɗa irin waɗannan bidiyoyi yana lalata tarbiyyar ƙananan yara. Yaro ko yarinya da bai kai ga sanin illar waɗannan abubuwa ba idan ya fara kallon irin wannan bidiyo, zuciyarsa za ta fara karkata zuwa ga fasiƙanci tun yana ƙarami. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake samun ƙaruwar lalata da rashin kunya a tsakanin matasa a yau. Abin da ake ɓoyewa a baya yanzu ya zama abin nunawa a fili saboda lalacewar kafofin sadarwa idan ba a yi amfani da su yadda ya dace ba.
Wani babban kuskure da matasa ke yi shi ne yarda da juna fiye da kima. Wasu ’yan mata suna ɗaukar saurayi tamkar miji, har su riƙa tura masa hotuna da bidiyoyin tsiraici cikin sirri. Amma idan soyayya ta lalace, wannan “sirri” na iya zama sanadin rugujewar rayuwarta. Sau da yawa saurayin kan yi amfani da wannan wajen yi mata barazana ko neman kuɗi. Idan ta ƙi, sai ya yaɗa bidiyon domin kunyata ta.
Haka nan akwai samarin da saboda son nuna isa ga abokai suke ɗaukar bidiyon budurwarsu suna nunawa wasu. Wannan rashin mutunci ne da rashin tarbiyya. Namijin kirki ba zai taɓa ɗaukar mutuncin mace wasa ba, balle har ya yaɗa abin da zai kunyata ta. Duk wanda ya aikata haka ya nuna rashin tsoron Allah da rashin imani.
Illar wannan ɗabi’a ba ta tsaya kan mutum ɗaya ba. Iyayen yarinyar da bidiyonta ya bazu su ma suna shiga damuwa da kunyatawa a cikin al’umma. ’Yan uwanta kan kasa fita cikin jama’a saboda tsoron abin da mutane za su ce. Wani lokaci ma ana samun rikici tsakanin iyalai saboda irin waɗannan abubuwa.
A bangaren addini kuma, yaɗa tsiraici yana daga cikin manyan hanyoyin yaɗa alfasha a cikin al’umma. Musulunci ya koyar da kare mutunci da suturta laifin mutane. Amma yau wasu suna ganin kamar daidai ne yaɗa bidiyon tsiraici don neman masu kallo ko samun farin jini a kafafen sada zumunta. Wannan babban kuskure ne. Duk wanda ya yaɗa irin wannan bidiyo yana samun zunubin duk wanda ya kalla ko ya ƙara turawa wani.
Haka kuma, akwai matsalar “blackmail” da ke ƙaruwa sakamakon irin waɗannan bidiyoyi. Wasu samari kan riƙa yi wa ’yan mata barazanar cewa idan ba su ci gaba da soyayya ba ko ba su ba su kuɗi ba, za su saki bidiyonsu a intanet. Wannan ya jefa mata da dama cikin tsoro da damuwa. Wasu ma saboda tsoron abin kunya suke ci gaba da zama cikin alaƙar da ba ta da amfani.
Dole ne iyaye su ƙara sanya ido kan tarbiyyar ’ya’yansu. A yau waya ta zama tamkar makaranta ce ga yara, saboda haka idan ba a kula ba, kafafen sada zumunta za su koya musu abubuwan da suka saɓa wa addini da al’ada. Iyaye su riƙa duba irin abokan da ’ya’yansu ke hulɗa da su da kuma abin da suke kalla a waya.
Malamai ma suna da rawar takawa wajen wayar da kai. Ya kamata a ci gaba da yin huɗubobi da nasihohi kan illar zina, tsiraici da rashin amfani da kafafen sada zumunta yadda ya dace. Matasanmu na buƙatar tarbiyya da faɗakarwa fiye da kowane lokaci.
Hukumomi kuma su ƙara ɗaukar matakan hukunta masu yaɗa bidiyon tsiraici da cin zarafin mutane a intanet. Bai kamata mutum ya ɗauki mutuncin wani ya mayar tamkar abin wasa ba. Idan aka tsaurara hukunci, hakan zai rage yawaitar irin wannan ɗabi’a.
Ga matasa kuwa, ya kamata su fahimci cewa soyayya ba hujja ba ce ta aikata abin da zai lalata rayuwa. Duk wani abu da mutum zai yi a yau ya kamata ya tuna cewa wata rana zai iya nadama. Bidiyon da aka ɗauka cikin minti ɗaya na iya zama abin kunya har tsawon rayuwa.
Ya zama wajibi mu dawo ga koyarwar addini da tarbiyyar gargajiya. Mutunci shi ne babban abin da mutum ke da shi. Idan ya lalace, yana da wahala a gyara shi. Don haka matasa su guji tura hotuna ko bidiyoyin tsiraici, su kuma nisanci duk wata hulɗa da za ta iya jefa su cikin nadama nan gaba.
Al’umma mai tarbiyya ita ce al’umma mai makoma. Idan muka bari tsiraici da fasikanci suka mamaye zukatan matasa, to muna gina al’umma ce da za ta rasa kunya, tsoron Allah da ɗabi’a ta gari. Wannan kuwa babban haɗari ne ga makomar iyalai da ƙasa baki ɗaya.
Allah Ya shiryar da matasanmu, Ya kare al’ummarmu daga fitintinu da lalacewar ɗabi’u.
Saƙo daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190. Mahdimusa84@gmail.com.

No comments