Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa akwai masu ba ’yan bindiga bayanai daga cikin gwamnati, hukumomin tsaro da kuma al’ummom...
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa akwai masu ba ’yan bindiga bayanai daga cikin gwamnati, hukumomin tsaro da kuma al’ummomin yankunan da abin ya shafa, lamarin da ke taimaka wa masu aikata laifuka wajen ci gaba da hare-harensu a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels Television, inda ya ce matsalar rashin tsaro a Katsina na ƙara ta’azzara saboda yadda wasu ke tona bayanan sirri na tsaro ga ’yan bindiga.
Raɗɗa ya ambaci wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Mohammed, yana mai cewa masu leƙen asiri daga cikin gwamnati da al’umma na taimaka masa wajen kauce wa kamawa tare da hana jami’an tsaro cimma nasara a ayyukansu.
“Wannan mutumin da ke addabar mu, mun san shi sarai. Sunansa Mohammed. Kowa ya san shi, an haifi mahaifinsa da kakanninsa a yankin nan. Amma matsalar ita ce al’umma ba sa bayar da sahihan bayanai. Wasu daga cikinsu ma suna taimaka masa,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa bayan mintuna kaɗan da kammala wani babban taron tsaro da aka yi a gidan gwamnatin jihar domin tsara matakan yaƙi da ’yan bindiga, mutumin ya riga ya samu bayanin duk abin da aka tattauna.
“Akwai masu ba shi bayanai daga cikinmu. Har ma ya ƙirƙiro wata sabuwar dabara inda yake tunzura wasu ƙauyuka su yi zanga-zanga a kan gwamnati domin a matsa mata lamba kada ta bi sawunsa,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa duk lokacin da jami’an tsaro suka shirya fita aiki bayan samun rahoton hari, wasu daga cikin al’umma kan yi wa ’yan bindigar gargaɗi tare da bayyana musu hanyoyin da jami’an tsaron za su bi, wanda hakan ke ba su damar kafa kwanton ɓauna.
“A wannan yanayi muke ciki yanzu. Akwai masu ba su bayanai daga cikinmu, daga cikin jami’an tsaro da kuma cikin al’umma,” ya jaddada.
Da yake magana kan batun sasanta wa da ’yan bindiga, Raɗɗa ya ce tun farko bai goyi bayan yin sulhu da masu aikata laifuka ba, amma daga baya wasu al’ummomi suka roƙi a ba su damar tattaunawa da su saboda tsananin hare-haren da suke fuskanta.
A cewarsa, mutanen yankunan sun bayyana cewa sun sha wahala matuƙa ba tare da samun isasshen kariya daga jami’an tsaro ba, don haka suka yi imanin cewa tattaunawa za ta iya dawo da zaman lafiya.
“Sun ce mini: ‘Mai girma gwamna, mun gana da su kuma sun nuna shirinsu na ajiye makamai. Mun sha wahala sosai ba tare da kariya ba. Don Allah ka ba mu damar yin sulhu idan hakan zai kawo zaman lafiya,’” in ji shi.
Gwamnan ya ce daga bisani ya amince al’ummomin su ci gaba da tattaunawar, amma shi da kansa bai shiga cikin shirin ba.
Ya bayyana cewa wasu ƙananan hukumomin da suka rungumi tsarin sasanta wa da ’yan bindiga sun shafe fiye da shekara guda ba tare da kai musu hari ba.
“Yanzu haka akwai wasu ƙananan hukumomi da suka yi sulhu da ’yan bindiga, kuma fiye da shekara guda ba a kai hari a wuraren ba. Mun samu zaman lafiya a mafi yawan yankunan da ake fama da hare-hare a baya,” in ji gwamnan.
Sai dai Raɗɗa ya nanata cewa ba zai fara neman sulhu da ’yan bindiga da kansa ba, amma idan su ne suka nemi zaman lafiya, zai iya tattaunawa da su daga matsayi na ƙarfi ba na rauni ba.

No comments