Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Duba Yiwuwar Sake Tsayawa Takara — Jonathan

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya ce har yanzu yana tuntuɓa kan ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Jonathan ya bayyan...





Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya ce har yanzu yana tuntuɓa kan ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Jonathan ya bayyana hakan ne lokacin da wata ƙungiyar matasa mai suna Coalition for Jonathan 2027 ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar da magoya bayansa, Jonathan ya jaddada muhimmancin kishin ƙasa, zaman lafiya da kuma shiga harkokin siyasa musamman ga matasa.

Ya nuna damuwa kan yadda yawan masu kaɗa ƙuri’a ke ci gaba da raguwa duk da ɗimbin mutanen da suka cancanci kaɗa ƙuri’a a Najeriya.

Jonathan ya buƙaci matasa su mallaki katin zaɓe tare da shiga harkokin siyasa maimakon taƙaita kansu ga tattaunawar siyasa kawai.

Da yake magana kan kiraye-kirayen da ake masa na ya sake tsayawa takara, tsohon shugaban ƙasar bai bayyana matsayarsa kai tsaye ba, amma ya ce har yanzu yana tunani sosai.

“Na ji abin da kuke cewa, kuma zan yi tunani sosai,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, takarar shugaban ƙasa ba wasa ba ce, yana mai cewa ba zai iya tashi kawai ya ce zai sake neman shugabancin ƙasa, ba tare da tunani ba.

“Ana buƙatar zaman lafiya da sahihin zaɓe a ƙasar nan. Idan babu zaɓe mai gaskiya da zaman lafiya, mutane nagari ba za su so shiga siyasa ba,” inji Jonathan.

Tun da farko, ƙungiyar ta buƙace shi da ya tsaya takara domin taimakawa wajen ceto ƙasar daga matsalolin da take fuskanta.

Sai dai Jonathan ya ce duk wanda ke son ganin canji dole ne ya shiga tsarin zaɓe ta hanyar rajista da mallakar katin zaɓe.

No comments