Hukumar Hisba a shiyyar Katagum ta jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata wani sabon salo na musayar mata...
Hukumar Hisba a shiyyar Katagum ta jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata wani sabon salo na musayar mata domin hulÉ—ar aure da jima’i a tsakanin su, a Azare cikin Æ™aramar hukumar Katagum.
Bayanan hakan ya fito ne daga bakin Kwamandan Hisba na shiyyar Katagum, Malam Ridwan Muhammad Khairan yayin zantawa da manema labarai a garin Azare, inda ya ce an cafke mutanen ne bayan samun Æ™orafe-Æ™orafe daga al’umma da wasu daga cikin ’yan Æ™ungiyar da ake kira “Wuddadu”.
A cewar Malam Ridwan “An kama waÉ—annan mutane ne bisa zargin shiga wata yarjejeniya inda suke musayar matansu domin hulÉ—ar aure da jima’i a tsakaninsu.”
Kwamandan ya Æ™ara da cewa, wannan É—abi’a ba ta da tushe a addinin musulunci, yana mai cewa: “Wannan aiki babu wata hujja a shari’ar Musulunci da ke goyon bayansa, duk da cewa wasu daga cikinsu sun yi Æ™oÆ™arin jingina shi da mafarki da É—aya daga cikinsu wai ya ce ya yi.”
Kwamandan na Hisba ya jaddada cewa, Hisba ba za ta lamunci duk wani abu da ya saÉ“a wa koyarwar addini da É—abi’un al’umma ba, yana mai gargaÉ—in cewa za su É—auki matakin doka kan duk wanda aka samu da aikata irin wannan aiki da ke da alaÆ™a da baÉ—ala.
Ya ce: “A Æ™arÆ™ashin shari’ar Musulunci, dole ne aure ya kasance an yi shi bisa Æ™a’ida tare da shaidu, kuma abin da waÉ—annan mutane suka aikata ya yi kama da zina kai tsaye.”
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar ta Wuddadu a Azare da ke ƙaramar hukumar Katagum, Malam Sagir Bashir ya ce sun shafe sama da shekara guda suna ƙoƙarin gyara halayen waɗanda abin ya shafa ta hanyar nasiha da jan kunne.
Ya ce: “Mun yi Æ™oÆ™ari sosai wajen hana wannan É—abi’a ta hanyar gargaÉ—i da ba su shawara, amma suna ci gaba da aikatawa a É“oye, wanda hakan ya tilasta mana kai rahoto ga Hisba domin kare mutuncin al’umma.”
Ya kuma bayyana cewa irin wannan abu ya taɓa faruwa a baya, inda aka gargaɗi waɗanda suke aikata laifin tare da alƙawarin daina wa, amma daga baya suka koma yin hakan.
A cewarsa: “Wannan É—abi’a ba ta cikin koyarwar addininmu, illa wasu daga cikinsu da suka yi iÆ™irarin cewa suna samun mafarki da ke goyon bayan hakan.”
.jpg)
No comments