Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AbdulSamad BUA Ya Zama Na Biyu Cikin Attajiran Afirka Bayan Wuce Johann Rupert

Shugaban kuma wanda ya kafa rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka bayan da ya wuce hamshaƙin...




Shugaban kuma wanda ya kafa rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka bayan da ya wuce hamshaƙin attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert.

Rahotanni sun nuna cewa hauhawar arzikin Rabiu na daga cikin mafi girman ƙarin dukiya da aka samu a duniya a bana, kamar yadda jadawalin attajirai na Bloomberg Billionaires Index ya bayyana.

Sabon jadawalin Bloomberg ya nuna cewa dukiyar Abdul Samad Rabiu ta kai dala biliyan 18.6, abin da ya sanya shi a matsayi na 138 cikin jerin attajiran duniya baki ɗaya.

Rahoton ya nuna cewa dukiyarsa ta ƙaru da kusan dala biliyan 8.47 tun daga farkon shekarar 2026 zuwa yanzu.

An bayyana cewa ƙarin darajar hannayen jarin kamfanoninsa na masana’antu ne ya taimaka wajen bunƙasar dukiyarsa cikin gaggawa.

Kafin wannan lokaci, an kiyasta dukiyar Rabiu ta kai kusan dala biliyan 15.9, lamarin da ke nuna irin saurin ci gaban da ya samu cikin ‘yan watannin nan.

A gefe guda kuma, jadawalin Bloomberg ya nuna cewa dukiyar Johann Rupert ta ragu zuwa dala biliyan 17.9 bayan da ya yi asarar kusan dala biliyan 1.76 a bana, abin da ya jefa shi zuwa matsayi na 153 a duniya.

Bayanan Bloomberg sun nuna cewa Abdul Samad Rabiu ne attajirin Afirka da ya fi samun ƙarin arziki a shekarar 2026, musamman ta hanyar kasuwancinsa na siminti, kayan abinci da masana’antu.

Sabon jadawalin ya bar Rabiu ne a bayan Aliko Dangote kaɗai cikin attajiran Afirka.

Binciken bayanan ya nuna cewa Aliko Dangote ya ci gaba da kasancewa mutum mafi arziki a Afirka, inda aka kiyasta dukiyarsa ta kai dala biliyan 34.4.

Dangote ya kasance a matsayi na 66 cikin attajiran duniya bayan da dukiyarsa ta ƙaru da kusan dala biliyan 4.38 a bana.

Har zuwa ranar 7 ga watan Mayu, jadawalin Bloomberg bai nuna wani ɗan Najeriya a cikin mutum 500 mafi arziki a duniya ba baya ga Dangote da Rabiu.

Jadawalin ya nuna cewa Mike Adenuga, wanda ya kafa kamfanin sadarwa na Globacom, yana da dukiyar da aka kiyasta ta kai dala biliyan 6.5, yayin da shugaban kamfanin Geregu Power Plc, Femi Otedola, ke da dukiyar kusan dala biliyan 1.3, amma duk da haka ba su shiga cikin jerin mutum 500 mafi arziki a duniya ba.

Rahoton ya kuma tuna cewa Femi Otedola ya sayar da mafi yawan hannun jarinsa a Geregu Power Plc kan kuɗi sama da tiriliyan 1.088 naira a shekarar 2025, a wata yarjejeniya da wasu bankuna ƙarƙashin jagorancin Zenith Bank Plc suka ɗauki nauyin kuɗinta.

Tun a watan Maris ɗin wannan shekara, mujallar Forbes ta bayyana Abdul Samad Rabiu a matsayin attajirin Afirka da ya fi samun ƙarin dukiya bayan da arzikin sa ya ƙaru da dala biliyan 6.1 cikin shekara guda.

Forbes ta ce dukiyar Rabiu ta haura da kaso 120 cikin ɗari, daga dala biliyan 5 zuwa dala biliyan 11.2, abin da ya ɗaga shi daga matsayi na shida zuwa na uku cikin attajiran Afirka a wancan lokaci.

No comments