Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana duba wasu hanyoyi d...
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana duba wasu hanyoyi domin tallafa wa kamfanonin jiragen sama na gida, musamman masu jigilar maniyyata, domin rage musu raɗaɗin tashin farashin man jirgi (Aviation Fuel) a kasuwannin duniya.
Ambasada Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026 da ke tafe. Ya ce hukumar tana tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin sufurin jiragen sama domin tabbatar da an gudanar da jigilar maniyyata cikin sauki da nasara.
Shugaban na NAHCON ya ƙaryata rahotannin da ke cewa wasu kamfanonin jiragen da aka ƙulla yarjejeniya da su suna nuna ɗar-ɗar wajen yin jigilar saboda tsadar mai. Ya bayyana waɗannan rahotanni a matsayin jita-jita kawai da ba su da tushe bare makama.
"Domin kauce wa kokwanto, dukkan shirye-shirye suna tafiya yadda ya kamata. Kuma muna sa ran fara jigilar farko ta mahajjata zuwa ƙasa Mai Tsarki ranar 3 ga watan Mayu, 2026."
Yusuf ya ƙara da cewa, shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya ke shirin yi na nufin samun maslaha ne ta bangarori biyu. Bangaren Kamfanoni don Tabbatar da cewa ba su tafka asara ba sakamakon tsadar mai, sai Bangaren Alhazzai dan Kare maniyyata daga biyan karin kudin jirgi mai nauyi.
A cewar sa, dukkan kamfanonin jiragen da aka amince da su sun sake jaddada aniyarsu ta gudanar da aiki cikin kwarewa da kiyaye lafiyar mahajjata, yayin da tattaunawa ke ci gaba da gudana tsakanin NAHCON da hukumomin kula da sufurin jiragen sama.
Duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, shugaban hukumar ya nuna ƙwarin gwiwar cewa jigilar mahajjatan zuwa Saudiyya da dawowar su gida Nijeriya zai gudana lami-lafiya ba tare da tangarɗa ba.

No comments