Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JIGILAR MAHAJJATA: Hukumar Jin Daɗin Alhazan Kaduna Ta Yi Sabuwar Bas Ta Zamani

  A ƙoƙarin ganin an kawo sauƙi wajen zirga- zirgar maniyyata a hajjin bana, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙara  bayar da sabuwa...

A ƙoƙarin ganin an kawo sauƙi wajen zirga- zirgar maniyyata a hajjin bana, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙara  bayar da sabuwar mota ƙirar bas mai kujeru 38, wacce ke amfani da iskar  (CNG), ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar.

Motar mai kujeru 38 tare da wuraren tsayawa guda 30, tana da damar ɗaukar fasinjoji har 68 a kowace tafiya, kuma ana sa ran za ta taimaka wajen inganta harkokin sufuri ga maniyyata, tare da ƙara inganci, tsaro da jin daɗi yayin jigilar su a lokacin aikin Hajji.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Uba Sani na tabbatar da jin daɗin alhazan jihar Kaduna, tare da ƙudirin samar da cikakken goyon bayan aiki domin ganin an gudanar da Hajji cikin sauƙi da nasara.

Hakan na zuwa ne bayan wasu gyare-gyare da aka yi a sansanin alhazai da ke Mando, ciki har da shimfida sabuwar hanya mai kwalta da kuma inganta gine-ginen sansanin domin samar da yanayi mai kyau ga maniyyata kafin tafiyarsu.

Da yake gabatar da motar a madadin gwamnatin jihar Kaduna, Daraktan Ayyuka na kamfanin Kaduna Line, Malam Muhammad Sagir, ya bayyana cewa wannan tallafi wata shaida ce ta jagoranci mai kishin jama’a da Gwamna Uba Sani ke nunawa, musamman wajen inganta ayyukan hidima ga al’umma.

A nasa ɓangaren, Daraktan Ayyuka na Hukumar jin daɗin Alhazai, Malam Abubakar Usman Yusuf, wanda ya karɓi motar a madadin Shugaban hukumar, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar, yana mai cewa wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar ƙarfafa ayyukan hukumar.

Ya kuma yaba da yadda gwamnatin ke amfani da sabbin hanyoyin sufuri masu amfani da iskar CNG, yana mai cewa hakan ya dace da ƙa’idojin duniya na kiyaye muhalli da inganta ayyukan gwamnati.

Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sake jaddada shirinta na samar da ingantattun ayyuka masu nagarta ga dukkan maniyyata, domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin tsari da aminci.
 

No comments