Daga Zubairu Lawal, Lafia Wasu 'yan Bindiga ɗauke da miyagun Makamai Sun kutsa kai makwancin ɗaliban Jami'ar Nasarawa a yankin Ninz...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Wasu 'yan Bindiga ɗauke da miyagun Makamai Sun kutsa kai makwancin ɗaliban Jami'ar Nasarawa a yankin Ninzo da ke garin Gudi a Daren jiya.
Ɗaliban Jami'ar Jihar da ke karatu a Bangaren Faculty of Engineering, da ke garin Gudi, Sun kasance cikin fargaba da tashin hankali.
Lamarin ya afku ne a ranar Laraba 6/5/2026 da misalin ƙarfe 9 na dare. Rundunar 'yan sandan Jihar ta tabbatar da faruwan lamarin cikin sanarwar da ta tura wa manema Labarai a Jihar.
'Yan Sanda Sun tabbatar da 'Yan Bindiga sun yi awon gaba da mutum bakwai ciki har da ɗaliban shida a cikin Daren.
Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin su ya kawo ziyara ne, amma lamarin ya rutsa da shi.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Nasarawa CP Shattima Jauro Mohammed ya kai ziyara kai tsaye wurin domin duba halin da ake ciki tare da tabbatar wa ɗalibai, mazauna yankin da kuma al’ummar jami’ar cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa domin ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Domin ƙarfafa ayyukan da ake yi, Kwamishinan ‘Yan Sandan ya sake tura Area Commander na Akwanga domin jagorantar ayyukan sintiri da bincike a yankin har sai an ceto waɗanda aka sace. Bugu da ƙari, an tura haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da ‘Yan Sanda, DSS, Sojoji, NSCDC, ƙungiyoyin vigilante da sauran jami’an musamman na rundunar domin ƙara ƙaimi wajen gano masu garkuwar.
Rundunar na kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura da tsaro tare da roƙon duk wanda ke da wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen gudanar da wannan aiki da ya sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wata hukuma ta tsaro cikin gaggawa

No comments