Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BABBAN LABARI: Tsauraran Matakai Da Ƙa'idojin Da CBN Ya Gindaya, Dangane Da Bashin Naira Tiriliyan 2.9 Da Kamfanin NESTOIL Ya Kasa Biyan Wasu Bankunan Nijeriya

  *Yadda katutun bashin ya jawo jinkirin raba ribar ƙarshen shekarar 2025 a wasu manyan bankuna  Kamfanin ɗanyen mai na NESTOIL mallakar att...

 

*Yadda katutun bashin ya jawo jinkirin raba ribar ƙarshen shekarar 2025 a wasu manyan bankuna 

Kamfanin ɗanyen mai na NESTOIL mallakar attajiri Ernest Obiejesi ya jefa wasu manya da ƙananan bankunan Nijeriya cikin halin ƙaƙanikayi, kwatagwangwama da jangwangwama, yayin da bashin naira tiriliyan 2.9 da bankunan ke bin sa suka maƙale, ake ta haƙilo da turnuƙun shari'ar neman yadda za a biya bashin a kotu.

Baya ga cukumurɗar shari'a da ake tafkawa, a ɗaya gefen kuma wasu manyan bankuna uku da suka fi bin Nestoil bashi mai tarin yawa, sun kasa biyan ribar ƙarshen shekarar 2025, sakamakon wasu tsauraran matakan da CBN ya gindaya na ƙin amincewa bankunan su raba ribar ga masu hannayen jari, har sai an tantace matsayar bashin da suka danƙara wa Nestoil Limited tukunna.


Manyan bankunan da suka fi Afkawa cikin wannan tsomomuwar basussukan Nestoil sun haɗa da United Bank of Africa (UBA) da kuma Access Bank a baya-bayan nan, waɗanda har yau ba su bayyana rabon ribar ƙarshen shekarar  2025 ba. Shi ma FCMB tuni ya afka cikin wannan jula-jula.

Sakamakon bayanan ƙididdigar ciniki da ribar shekarar 2025 na UBA ya nuna asarar kuɗi daga tanadin bashin da ya kai Naira biliyan 331, yayin da asarar da Access Holdings ya yi wajen rage darajar rance (impairment) ta ƙaru da kashi 209, zuwa Naira biliyan 287.3.

Jimillar bashin da bankunan Nijeriya suka bayar ga ɓangaren hadahadar mai da iskar gas zuwa ƙarshen 2024 ya kai Naira tiriliyan 21, inda manyan bankunan da suka fi hulɗa da Nestoil suka haɗa da UBA, First Bank, Access Bank, FCMB, Union Bank, Ecobank da kuma African Export-Import Bank.


Tsauraran Matakan da CBN Ya Ɗauka Kan Nestoil da Bankunan da Suka Danƙara wa Kamfanin Bashi:

A ƙarƙashin tsauraran matakan, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, Babban Bankin Nijeriya ya hana waɗannan bankuna biyan ko raba ribar ƙarshen shekara-shelara, har sai sun kammala tanadin dukkan basussukan da ba a biya ba.

A ranar 13 ga Yuni, 2025 dai CBN ya hana bankunan da abin ya shafa su raba ribar ƙarshen shekara-shekara, kamar yadda wata sanarwar da aka fitar, mai ɗauke da sa-hannun Daraktan Kula da Mu'amalar Bankuna, Dakta Olubokola A Akinwunmi.

Yanayin Bashin Nestoil:

Matsalar bashin bankunan yanzu ta ta’allaƙa ne kan rashin ikon Nestoil wajen biyan basussukan haɗin gwiwa da aka ba kamfanin, a lokacin da ake sa ran ƙarin samar da mai.

Rashin biyan bashin da Nestoil ke yi ya ƙara matsin-lamba ga bankuna, musamman waɗanda suka fi hulɗa da kamfanonin mai masu zaman kan su.

Baya ga tanadin asarar bashin, bankuna na ƙoƙarin karɓo bashin nasu.
Masu bada rance sun samu umarnin kotu a watan Oktoban 2025, wanda ya riƙe kadarorin Nestoil—ciki har da kuɗaɗen banki, gidaje da kayayyakin mai—a fiye da bankuna 20.

Ana ci gaba da ƙoƙarin karɓar kadarori duk da ƙalubalen shari’a da ake fuskanta daga Nestoil.

Bankuna na shirin ƙwace kadarori, gidaje da kayan mai, wanda zai iya haifar da dogon rikicin shari’a da zai kulle kuɗaɗe masu muhimmanci, tare da barazana ga wadatar kuɗi a fannin banki.


Barazanar Bashin Nestoil ga Tsarin Banki:

Masana na gargaɗin cewa dawo da waɗannan kuɗaɗe ba zai zama mai sauƙi ba.
CBN yanzu ya fifita kare jarin bankuna, ta hanyar hana biyan ribar ƙarshen shekara-shelara har sai basussukan da ba a biya ba sun sauka ƙasa da kashi 5.

Adadin basussukan da ba a biya ba a fannin banki ya kusa kai kashi 7 a 2025, wanda ke barazana ga daidaiton bankuna idan matsalar bashin mai ta ci gaba.


Muhimmancin Matakin da CBN ya Ɗauka:

Ko da yake dakatar da raba ribar ƙarshen shekara-shelara yana cutar da masu hannun jari, masana na ganin cewa wannan tsauraran mataki na da muhimmanci domin kauce wa irin matsalar rushewar bankuna ta 2009.

Saboda haka hanyar tilasta bankuna su bayyana asara yanzu, CBN na tabbatar da cewa bashin Naira tiriliyan 21 da aka bai wa ɓangaren mai yana bayyana gaskiya, maimakon ɓoye shi.
Wannan matsin lamba daga ɓangaren mai na zuwa ne a daidai lokacin da aka kammala shirin ƙara jarin bankuna, wanda ya taimaka musu su iya ɗaukar irin wannan asara.


Yadda Nestoil Ya Ci Bashin Naira Tiriliyan 2.9:

Bashin Nestoil na Naira Tiriliyan 2.9 ba a lokaci ɗaya kamfanin ya ciwo shi ba. Ya taru ne tsawon shekaru yayin da kamfanin ke faɗaɗa ayyukan sa a yankin Neja Delta, inda ya riƙa karɓar rancen maƙudan kuɗaɗe, bisa tsammanin samun kuɗaɗen shiga daga man fetur, wanda hakan bai da bai tabbata ba.

A watan Disamba 2022, wani rukuni na bankuna 16 ƙarƙashin jagorancin FBN Group tare da Afreximbank suka haɗa bashin cikin wata yarjejeniya mai suna “Global Facilities” ƙarƙashin dokokin Ingila.

Waɗanda suka bayar da garanti sun haɗa da Neconde Energy, Obiejesi da kansa da matar sa Nnenna Obiejesi. A watan Oktoba 2025, an bayyana bashin ya kai sama da dala biliyan 1.01 da kuma naira biliyan 430 na daban.

A watan Oktoba 2025, wata kotu a Legas ta bayar da umarnin riƙe kadarorin Nestoil da Neconde Energy a bankuna sama da 20, ciki har da asusun banki, kadarori da kaya na mai. An kuma naɗa mai kula da kadarorin.

An samu rikicin shari’a kan wanda ke da ikon naɗa lauyoyi. A farko kotun ɗaukaka kara ta bai wa masu kuɗin iko, amma a ranar 10 ga Afrilu 2026, Kotun Koli ta soke hukuncin tare da sukar Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Yanzu ana sa ran shari’ar za ta koma kotun farko, kuma masana na ganin za ta iya ɗaukar shekaru saboda rikitarwa.


Ba Nestoil Ya Haddasa Jinkirin Raba Ribar Ƙarshe Shekara a Wasu Bankuna Ba -Nestoil:

A ranar Talata kamfanin mai na Nestoil ya fito ya ƙaryata labarin da yawancin jaridu suka buga a ranar Litinin, mai ɗauke da cewa "Bashin Naira Tiriliyan 2.9 da Nestoil ya kasa biyan bankuna, ya haifar da jinkirin biyan ribar ƙarshen shekara-shekara a wasu manyan bankuna uku."

Sanarwar ta yi zargin cewa Shugaban Bankin First Bank ya ɗauki nauyin wasu jaridu suka buga labarin.

Sai dai kuma ana ganin cewa wannan bayani na Nestoil ba gamsasshe ba ne, domin kamfanin ya kasa yin bayani kan naira tiriliyan 2.9 da bankunan ke bin sa bashi, lamarin da ake ci gaba da tafka shari'a kan waɗannan maƙudan kuɗaɗe.

A kan haka ne Nestoil ya ce bankunan sun ƙi raba ribar ce, wato 'dividends', saboda bin umarnin CBN, amma ba laifin Nestoil ba ne.

Hoto: Ernest Obiejesi, Shugaban Nestoil

No comments