Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Ɗaure Alƙali Kan Karɓar Cin Hanci A Gombe

Wata Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa Alkali Mohammad Suleiman Kumo, hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi bisa samun sa da laifin karɓar...




Wata Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa Alkali Mohammad Suleiman Kumo, hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi bisa samun sa da laifin karɓar cin hanci na Naira miliyan ɗaya.

Mai Shari’a H.H. Kereng, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata a Gombe.

An gurfanar da Kumo a gaban kotu a ranar 3 ga Disamba, 2025, kan tuhume-tuhume uku na cin hanci da Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) reshen Gombe ta gabatar.

Takardar tuhumar ta nuna cewa, yayin da yake aiki a matsayin Alkalin Lardi a Pantami, ya karɓi Naira miliyan ɗaya ta hanyar asusun Bankin Zenith na wani mai suna Adamu Ahmed, wanda ke aiki a matsayin rajistara a kotunsa, a ranar 6 ga Nuwamba, 2024.

Laifin, kamar yadda aka bayyana, ya saɓa da Sashe na 10(a)(i)(ii) na Dokar Hana Cin Hanci da Rashawa ta shekara ta 2000.

Da farko, wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa. Sai dai a ranar 30 ga Disamba, 2025, lauyansa, Adamu Bawa, ya shigar da ƙorafi yana ƙalubalantar ikon kotun sauraron shari’ar, yana mai cewa ya kamata a miƙa batun ga Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a (JSC).

Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara, A. Aliyu, ya yi watsi da wannan hujja, yana mai cewa Alƙali ba ya cikin jerin “judicial officers” kamar yadda Sashe na 318(1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka gyara) ya tanada.

A hukuncin da ya yanke a ranar 17 ga Fabrairu, 2026, Mai shari’a Kereng ya yi watsi da ƙorafin, inda ya tabbatar da cewa kotun na da hurumin sauraron shari’ar.

A zaman kotu na ranar 5 ga Mayu, 2026, lauyan wanda ake tuhuma ya sanar da kotu cewa abokin cinikinsa yana son sauya matsayinsa daga musanta zargi zuwa amincewa da laifin.

Bayan sake karanta tuhume-tuhumen, Kumo ya amsa laifinsa. Bayan haka, masu gabatar da ƙara suka roƙi kotu da ta same shi da laifi tare da umartar ya biya Naira 500,000 a matsayin diyya ga kuɗaɗen bincike da shari’a.

A hukuncinsa, Mai shari’a Kereng ya bayyana laifin a matsayin mai tsanani, inda ya same shi da laifi bisa dokar da ta dace.

Ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi tare da zaɓin biyan tara ta Naira 250,000. Haka kuma kotun ta umarce shi da ya biya Naira 500,000 ga EFCC a matsayin diyya.

Lamarin ya samo asali ne daga korafe-korafen da wasu mutane biyu, Abubakar Isa Jauro Kuna da Suleiman Haruna, suka gabatar, wanda ya kai ga bincike, gurfanarwa da kuma hukuncin da aka yanke masa.

No comments