Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Samu Tsohon Ministan Lantarki Da Laifin Almundahanar Naira Biliyan 33.8

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da laifin halasta kuɗaɗen haram har naira biliya...



Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da laifin halasta kuɗaɗen haram har naira biliyan 33.8.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya ce Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC ta tabbatar da tuhume-tuhume 12 da ake yi wa tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta bayyana cewa, daga cikin jerin laifukan, an karkatar da kuɗin aikin wutar lantarki na Zungeru da Mambilla na aƙalla Naira biliyan 22 ta hannun wanda ake tuhuma da wasu na kusa da shi.

Alƙalin ya ce ɓangaren kariya bai gabatar da gamsassun hujjoji da za su rusa bayanan masu gabatar da ƙara ba, saboda haka kotun ta same shi da laifi a tuhuma ta farko.

Rahotanni sun ce Saleh Mamman wanda ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari bai halarci zaman kotun a lokacin yanke hukuncin ba.

Tun dai a shekarar 2021 ce aka cafke Saleh Mamman, watanni huɗu bayan tsohon shugaban ƙasa Buhari ya sauke shi daga muƙamin.

No comments