Aƙalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 254 suka kamu da cutar sankarau bayan ɓarkewar annobar a ƙananan hukumomi tara na jiha...
Aƙalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 254 suka kamu da cutar sankarau bayan ɓarkewar annobar a ƙananan hukumomi tara na jihar Sokoto.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato, Faruk Abubakar-Wurno, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba, inda ya ce annobar ta bazu a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya tilasta gwamnati ɗaukar matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar.
Ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka mutu sun rasu ne a gidajensu kafin jami’an gwamnati su kai ɗauki, saboda wasu mazauna yankunan sun ɗauki cutar a matsayin wani abu na al’ajabi ko na ruhi, abin da ya janyo jinkirin neman magani a asibitoci.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta buɗe cibiyoyin killace masu cutar a garuruwan Dogondaji da Kurawa da ke ƙananan hukumomin Tambuwal da Sabon Birni domin kula da masu ɗauke da cutar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa mutane 201 da aka kwantar a cibiyoyin lafiya mallakin gwamnati sun samu sauƙi kuma an sallame su bayan an yi musu magani.
Ya bayyana ƙananan hukumomin da annobar ta fi shafa da yawan waɗanda suka kamu kamar haka: Dange-Shuni mutum 26, Kebbe 16, Shagari 51, Tambuwal 34, Wamakko 60, Sabon Birni 63, Bodinga biyu, Kware biyu, yayin da Gada ke da mutum ɗaya.
Dangane da sakamakon binciken gwaje-gwaje, Abubakar-Wurno ya ce an aika samfurori domin tantancewa, inda aka tabbatar da mutum takwas sun kamu da cutar sankarau, duk da cewa wasu sakamakon sun nuna babu cutar.
Ya ce gwamnati ta ƙara wayar da kai ga al’umma tare da ba mazauna yankunan shawarar su riƙa kwana a ɗakuna masu isasshen iska ko kuma a wajen gidaje domin rage yaduwar cutar, musamman ganin yadda tsananin zafi ke taimakawa wajen bazuwar ta.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa yara masu shekaru tsakanin shekara ɗaya zuwa 15 su ne suka fi kamuwa da cutar a wannan karo.
Ya yi gargaɗin cewa cunkoson jama’a da iskar damina mai bushewa sun ƙara haɗarin yaduwar cutar, abin da ke ƙara barazana ga lafiyar al’umma musamman a jihohin Arewa.
Haka kuma ya ce gwamnatin jihar ta ƙarfafa aikin sa ido ta hannun jami’an kula da cututtuka, tare da samar da magunguna, gwaje-gwaje da kuma bunƙasa ƙarfin dakunan bincike domin gano masu ɗauke da cutar cikin gaggawa.

No comments