Sabon Ministan Wutar Lantarki, Olasunkanmi Tegbe, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta kawo ƙarshen yawaitar faɗuwa...
Sabon Ministan Wutar Lantarki, Olasunkanmi Tegbe, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta kawo ƙarshen yawaitar faɗuwar tsarin rarraba wutar lantarki na ƙasa, matsalolin rashin tabbatacciyar wuta da kuma lalata kayayyakin lantarki da masu ɓarna ke yi a faɗin ƙasar nan.
Tegbe ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin tantancewarsa a zaman Majalisar Dattawa da aka gudanar a Abuja, inda daga bisani majalisar ta tabbatar da naɗinsa a matsayin Ministan Wutar Lantarki bayan yi masa tambayoyi kan halin da ɓangaren lantarki ke ciki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya jagoranci zaman tantancewar, inda sanatoci suka matsa masa lamba kan ya bayyana takamaiman lokacin aiwatar da gyare-gyare, gaskiya da kuma cikakken tsarin da zai tabbatar da daidaituwar samar da lantarki tare da dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari.
Majalisar ta kuma ɗora masa alhakin kawo sauye-sauye cikin gaggawa a wani ɓangare da ya daɗe yana fama da matsalolin faɗuwar grid, raunin tsarin isar da wuta da kuma matsanancin ƙarancin kuɗaɗe da ya kai tiriliyoyin naira.
Sanatoci daga ɓangarori daban-daban sun bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun gaji da alkawura marasa cika, suna mai jaddada cewa dole sabon ministan ya nuna sakamako a cikin ‘yan watanni kaɗan ko kuma ya rasa amincewar jama’a.
Sanata Mohammed Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa ya bayyana cewa naɗin Tegbe ya zo a lokacin da ya dace, amma ya ce matsalolin da suka dabaibaye ɓangaren lantarki na buƙatar matakan gaggawa da tsauri.
Ya koka kan yadda faɗuwar grid ta zama ruwan dare, yana mai cewa hakan na hana bunƙasar masana’antu a Nijeriya. Ya kuma ɗora laifi kan gazawar tsarin isar da wuta wanda ya ce yana hana rarraba isasshiyar wutar da ake samarwa.
“Faɗuwar grid ta zama tamkar al’ada, lamarin da ke hana ci gaban ƙasa. Tsarin isar da wuta bai dace da ƙarfin samar da lantarki ba,” in ji shi.
Da yake mayar da martani, Tegbe ya amince cewa matsalolin ɓangaren lantarki sun yi zurfi kuma ba matsaloli ne na wucin gadi ba. Ya danganta hakan da rashin haɗin kai, gazawar bin ƙa’idojin fasaha da kuma ƙarancin iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da lantarki.
“Faɗuwar grid ba hatsari ba ne kawai, tana nuna akwai manyan matsaloli a tsarin,” in ji sabon ministan.
Ya yi alƙawarin aiwatar da wasu gyare-gyare cikin kwanaki 100 domin daidaita tsarin lantarki tare da ƙaddamar da wata manhajar bayyana ayyuka ga jama’a domin ‘yan Nijeriya su riƙa bibiyar ci gaban da ake samu.
“Idan babu sakamako cikin watanni uku, to babu shi cikin watanni shida. Ina roƙon ‘yan Nijeriya su ɗora mana alhaki,” in ji Tegbe.
Ministan ya kuma bayyana cewa akwai wasu mutane da ke cin moriyar gazawar tsarin lantarki, yana mai alƙawarin fuskantar duk wani yunƙurin zagon ƙasa.
“Akwai waɗanda ba sa son tsarin ya yi aiki saboda suna amfana da gazawarsa. Za mu yaƙe su,” ya ce.
Dangane da lalata kayayyakin lantarki, Tegbe ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga tsaron ƙasa, yana mai cewa za su yi aiki tare da jami’an tsaro, ciki har da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro da kuma rundunar sojoji domin kare muhimman kayayyakin lantarki.
Ya kuma amince cewa ɓangaren lantarki na fama da matsanancin ƙarancin kuɗaɗe da ya kai kusan naira tiriliyan shida, lamarin da sanatoci suka ce ya rage zuba jari tare da durƙusar da tsarin lantarki baki ɗaya.
A cewarsa, tsarin kuɗin lantarki na yanzu ba zai iya dorewa ba, saboda haka gwamnati za ta yi gyare-gyare ciki har da farashin lantarki da zai dace da yanayin kasuwa tare da la’akari da talakawa masu ƙaramin ƙarfi.
“Farashin lantarki dole ya dace da yanayin kasuwa, amma dole mu tabbatar da sauƙi ga talakawa,” in ji shi.
Sanatoci da suka haɗa da Tokunbo Abiru mai wakiltar Lagos ta Gabas sun nemi sabon ministan ya bayyana takamaiman lokacin da za a samu ingantacciyar lantarki, suna mai cewa wutar lantarki mai ɗorewa tana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.
Shi kuwa Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa ya soki rabon ɓangaren lantarki zuwa kamfanonin samarwa, isarwa da rarrabawa, yana mai cewa rashin haɗin kai tsakanin su ne ya ƙara dagula matsalar.
Tegbe ya tabbatar wa majalisar cewa tsarin gyaransa zai mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin sassan lantarki, inganta samar da iskar gas ga kamfanonin samar da wuta da kuma hanzarta samar da mitoci a faɗin ƙasa domin rage cajar ƙiyasta.
Game da samar da lantarki a karkara, ministan ya ce gwamnati za ta faɗaɗa amfani da ƙananan grid da makamashi mai sabuntawa musamman hasken rana domin kai wuta zuwa yankunan da ba su da isasshen lantarki.
“Makamashin da ba ya dogara da babban grid zai taimaka wajen kai lantarki ga yankunan da aka manta da su,” in ji shi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jaddada muhimmancin gyaran ɓangaren lantarki, yana mai cewa shi ne babban ƙalubalen da ke hana Nijeriya gogayya a fannin tattalin arziƙi.
“Masana’antunmu ba za su bunƙasa ba tare da ingantacciyar lantarki ba. Abin da muke buƙata yanzu shi ne sakamako, ba alkawura ba,” in ji Barau.
Duk da tsauraran tambayoyin da aka yi masa, sanatoci sun nuna kwarin gwiwa a kan ƙwarewar Tegbe da kuma tsarinsa na kawo gyara.
A jawabin rufe zaman, sabon ministan ya sake jaddada aniyarsa ta kawo sauyi mai ma’ana, yana mai cewa duk da girman ƙalubalen, ana iya samun ci gaba idan aka yi aiki da gaskiya, tsari da haɗin kai.
“Wannan aiki ne mai wahala, amma za a samu nasara idan aka yi aiki cikin gaskiya da haɗin kai. ‘Yan Nijeriya za su ga sauyi,” in ji shi.

No comments