Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Taron NASIDA: An Bayyana Samun Sama Da Dala Biliyan 2 Na Zuba Jari, Tare Da Samar Da Ayyukan Yi 50,000

Daga Zubairu Lawal, Lafia An ƙaddamar da Taron Zuba Jari na 2026 a jihar Nasarawa a ranar Laraba, inda aka bayyana cewa an samu nasarar sama...

Daga Zubairu Lawal, Lafia

An ƙaddamar da Taron Zuba Jari na 2026 a jihar Nasarawa a ranar Laraba, inda aka bayyana cewa an samu nasarar samar da Dala Biliyan 2, tare da ayyukan yi sama da 50,000.

Taron ya mayar da hankali sosai kan tabbatar da ɗorewar gyare-gyare ta hanyar hukumomi, yayin da Gwamna Abdullahi Sule, da  Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari na Tarayya suka jaddada bukatar ci gaba da manufofi bayan sauyin siyasa na 2027.

Taron na kwanaki biyu, mai taken Sauye-sauye Masu Ƙarfi: Gina Tarihi da Makoma Mai Dorewa, shi ne karo na uku tun bayan fara shirin a 2022. 

Wannan na zuwa ne yayin da Hukumar Kula da Ci gaban Zuba Jari ta Nasarawa (NASIDA) ta bayyana cewa an samu sama da dala biliyan 2 na zuba jari, tare da samar da ayyukan yi sama da 50,000 a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Da yake jawabi a madadin Gwamnatin Tarayya, Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yabawa Nasarawa bisa zama cibiyar haduwar masu zuba jari, masu tsara manufofi da abokan hulɗar ci gaba.

Ya ce taken taron yana nuna ainihin gwajin shugabanci: “ba wai yabon da ake yi masa a yau ba ne, amma irin gudunmawar da zai bayar a gobe.”

Shettima ya danganta ci gaban Nasarawa da gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa Nijeriya ta tashi daga hanyar faɗawa matsin tattalin arziki a 2023 zuwa samun ci gaban GDP na kashi 3.87% a 2025, raguwar gibin kasafin kudi zuwa kashi 3.0% na GDP, da kuma samun rarar ma’aunin biyan kudade na dala biliyan 6.83. 

Ya kuma ce ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru daga dala biliyan 3.99 a karshen 2023 zuwa sama da dala biliyan 46 a 2025.

Ya yabawa Nasarawa kan kafa NASIDA, cibiyar zuba jari ta One-Stop, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jiha da kuma Filin More Rayuwa (Infrastructure Park), yana mai cewa wadannan su ne ginshikan dorewar wadata. 

Ya ƙara da cewa manyan ayyukan tarayya kamar bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano za su kara tallafa wa shirin gas na jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce taron 2026 shi ne na karshe a karkashin gwamnatinsa, kuma wata muhimmiyar dama ce ga alkiblar tattalin arzikin jihar.

 Ya bayyana shi a matsayin “dandamali na dabaru don karfafa nasarorin da aka samu da kuma tsara hanyar gaba don sauyin tattalin arziki.”

Sule ya tuna cewa taron 2022 ya gabatar da arzikin albarkatun kasa na Nasarawa da kusancinta da Abuja ga masu zuba jari, yayin da na 2024 ya mayar da hankali kan noma, hakar ma’adinai, masana’antu da ababen more rayuwa.

A cewarsa, taron na bana an tsara shi ne domin kare gyare-gyare da dasa su cikin hukumomi masu dorewa, domin ci gaba ya wuce zamanin shugabanni Masu zuwa.

“Babban damuwa shi ne sauyin siyasa na iya haifar da rashin tabbas ga masu zuba jari, musamman idan gyare-gyare sun ta’allaka ne ga mutum daya maimakon tsari na hukumomi,” in ji Sule.

 “Don kiyaye amincewar masu zuba jari, dole ne a nuna cewa manufofi da tsarin doka da yarjejeniyoyi za su ci gaba da zama masu tabbas.”

Gwamnan ya ce wannan zai tabbatar wa masu zuba jari cewa jarinsu zai kasance cikin tsaro komai wanda ya gaje shi.

“Masu zuba jari suna son tabbacin cewa ko da babu Abdullah Sule, jarinsu zai kasance cikin tsaro kuma za a cigaba da manufofi,” in ji shi.

Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwale, ta ce Nasarawa ta zama abin koyi wajen yadda dorewar gyare-gyare ke jawo zuba jari. 

Ta bayyana GDP na jihar da kusan dala biliyan 12, tare da dala miliyan 800 a fannin ma’adinai, dala miliyan 400 a sarrafa sinadaran ( earth, ) da kuma wasu ayyuka masu kusan dala biliyan 1 a gaba.

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne yanayin kasuwanci—dole ne a samu tabbaci, daidaito da dorewa,” in ji ta.

Manajan Daraktan NASIDA, Ibrahim Adamu Abdullahi, ya ce gyare-gyaren da aka aiwatar sun kawo sauye-sauye sama da 50 a muhallin kasuwanci, ciki har da daidaita haraji,  tsarin dokar PPP mai karfi, da sabuwar Hukumar Wutar Lantarki ta Jiha. 

Ya ce hakan ya kara kuɗaɗen shiga na cikin gida daga naira biliyan 7 a 2019 zuwa naira biliyan 37 a 2025, tare da sanya Nasarawa cikin jihohin Najeriya 10 mafi saukin kasuwanci.

Sashen ƙulla yarjejeniyoyi (Deal Room) na taron na nuna ayyuka takwas da suka shirya don zuba jari, ciki har da cibiyar noma ta Gudi, cibiyar fasaha a Technology Village, kananan ayyukan wutar ruwa a Farin Ruwa da Dam din Doma, cibiyoyin sarrafa zinariya da lithium, asusun ababen more rayuwa na naira biliyan 100, cibiyar samar da wutar lantarki, da hanyar baya ta Akwanga-Panda-Yanyanya.

Abdullahi ya ce an kammala dukkan bincike na yiwuwar ayyukan, tare da tsara tsarin hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP), kuma kungiyoyin ayyukan suna shirye su tattauna da masu zuba jari.

Ya karkare da cewa: “Kowane zamani yana da manufa da ya kamata ya gano ya cika ko ya kasa. Babbar daraja ce a gare mu mu sanya Nasarawa ta zama mai gogayya da kuma mai jan hankalin masu zuba jari. 

Jarinku yana cikin tsaro inda gwamnati take da gaskiya, kuma hakan yana samuwa a Jihar Nasarawa karkashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule.”

 

No comments