Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BIDIYO: Aikin Sabon Titin Sakkwato–Badagry Ya Kankama

  A ci gaba da ziyarar duba ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma, tawagar Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagor...


 
A ci gaba da ziyarar duba ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma, tawagar Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Hulɗa da Jama’a, Mista Sunday Dare, ta ziyarci aikin sabon titin Sakkwato–Badagry da ake ginawa da kankare a Jihar Kebbi domin duba yadda aikin ke gudana.

Titin mai tsawon kilomita 1,068 na daga cikin manyan sabin ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, kuma a halin yanzu an kammala fiye da kilomita 30 na aikin.

Ziyarar ta gudana ne a ranar 6 ga Mayu, 2026.

No comments