Ministan Abuja Nyesom Wike ya kare gina gidajen da gwamnati ta yi wa alƙalai da sauran ma'aikatan ɓangaren shari'a a Abuja, inda ya ...
Ministan Abuja Nyesom Wike ya kare gina gidajen da gwamnati ta yi wa alƙalai da sauran ma'aikatan ɓangaren shari'a a Abuja, inda ya yi watsi da damuwar da ƙungiyoyin lauyoyi ta nuna cewa hakan zai iya shafar ’yancin ɓangaren shari'a.
Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake zagayen duba ayyukan da ake yi na gina gidajen alƙalai da gyara da sauran ababen more rayuwa domin amfanin ma'aikatan ɓangaren na shari'a a Abuja.
Jawabin na minista na zuwa ne bayan ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya, NBA ta soki abin da ta kira yunƙurin katsalandan daga ɓangaren zarwasta na samar da ababen more rayuwa ga ɓangaren shari'a.
Wike ya ce tallafin gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa ga alƙalai da sauran ma'aikatan shari'a ba sabon ba ne, kuma ba zai taɓa martabar ’yancin shari'a ba.
"Domin gwamnati ta yi gine-gine, hakan ba ya nufin za ta riƙa katsalanda a kan harkokin shari'a," in ji shi.
"A baya gwamnati ta gina gidaje ga majalisun tarayya da ma'aikatan shari'a. Ita kanta Kotun Ƙolin ai gwamnati ce ta gina. Don haka wannan ba sabon abu ba ne."

No comments