Ƙasashen Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar ƙara zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, yaƙi da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman laf...
Ƙasashen Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar ƙara zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, yaƙi da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026.
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka, inda ya gana da manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar. A yayin ziyarar, Ribadu ya isar da saƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen ɗorewar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ribadu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio da Sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaro na ƙasar Amurka.
Babban maƙasudin wannan ganawa shi ne duba yadda za a inganta raba bayanan sirri da kuma karfafa ayyukan soji na hadin gwiwa. NSA Ribadu ya jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Sahel, musamman Ayukan ta’addanci da tsagera, Safarar miyagun ƙwayoyi da makamai da Laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.
Hukumomin Amurka sun jinjina wa Nijeriya a matsayin ta na jagora a yankin Afirka, musamman wajen jagorantar yaki da ta'addanci a tafkin Chadi.
A nata bangaren, Nijeriya ta bayyana cewa tana amfani da dabarun karfin soja da kuma tattaunawa da inganta rayuwar jama'a don magance tushen matsalar rashin tsaro.
"Nijeriya tana godiya ga Amurka bisa taimakon da take bayarwa a bangaren horar da jami'ai, ba da bayanan sirri, da kuma tallafin jin ƙai." — Ribadu
A ƙarshen taron, bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntubar juna akai-akai ta hanyar haɗin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla sun fara aiki yadda ya kamata.

No comments