Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tarayyar Turai Ta Bi Sahun Hukumar FATF, Ta Cire Nijeriya Daga Jerin Ƙasashen Da Ke Da Haɗarin Safarar Kuɗi

Daga Ashafa Murnai Sakamakon gyare-gyaren kasuwar canjin kuɗi da bin ƙa’idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi, a yanzu haka Kungiyar ...



Daga Ashafa Murnai

Sakamakon gyare-gyaren kasuwar canjin kuɗi da bin ƙa’idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi, a yanzu haka Kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi.

Cikin wata sanarwar da Tarayyar Turai (EU) ta fitar a shafin ta na soshiyal midiya, ta bayyana cewa an cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi da tallafa wa ta’addanci, ta nuna irin gagarumar ribar da gyare-gyaren da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar suka haifar.

Wannan mataki ya nuna ƙaruwar bayyana gaskiya da bin ƙa’idoji a ɓangaren ayyukan kuɗi, tare da ingantaccen aiwatar da matakan yaƙi da safarar kuɗi da hana tallafa wa ta’addanci (AML/CFT).

Tunda an tsame sunan Nijeriya daga jerin ƙasashen da EU ke ganin suna da haɗari ana sa ran hakan zai ƙara wanzar da amincewa da haɗin gwiwa daga ƙasashen duniya ga tattalin arziƙin cikin gida.

Ɓangaren harkokin kuɗi na Nijeriya ya samu sauye-sauye masu yawa a ‘yan shekarun nan sakamakon gyare-gyare da aka aiwatar. Waɗannan sun haɗa da kasuwannin canjin kuɗi zuwa tsari guda, ƙara tsauraran ƙa’idoji da jagoranci, bayyana gaskiya a harkokin kasuwar musayar kuɗaɗen waje, da kuma ƙarfafa sa-ido kan zirga-zirga da tasarifin kuɗi a cikin tattalin arziki.

Yawancin waɗannan manufofi da gyare-gyare sun haifar da muhimman fa’idoji ga tattalin arziƙin ƙasa.
Babbar nasara daga cikin waɗannan ita ce cire Najeriya daga jerin ƙasashen da EU ke ɗauka a matsayin masu haɗari wajen safarar kuɗi da tallafa wa ta’addanci, tare da Afirka ta Kudu da wasu ƙasashen Afirka huɗu. 

Masana harkokin tattalin arziƙi sun bayyana wannan mataki a matsayin abin da zai ƙara ƙarfafa damar bunƙasar tattalin arziƙin Nijeriya.

Wata sanarwa da Kungiyar Tarayyar Turai ta wallafa a shafinta ta ce:
“Hukumar Tarayyar Turai, bayan tantancewa, ta kammala cewa Nijeriya ta ƙarfafa ingancin tsarin ta na yaƙi da safarar kuɗi da hana tallafa wa ta’addanci, tare da gyara matsalolin fasaha da dabaru da FATF ta bayyana a baya.

Wannan mataki ya yi daidai da shawarwarin da Hukumar FATF ta yanke a tarurrukan ta na watan Yuni da Oktoba na shekarar 2025, inda aka cire wasu ƙasashe daga jerin ‘Ƙasashen da ake sa ido na musamman’, wato waɗanda ake baya-baya da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga ranar 29 ga Janairu, 2026, za a daina amfani da tsauraran matakan bincike na musamman kan mu’amaloli da suka shafi Nijeriya da sauran ƙasashen da aka cire daga jerin, muddin Majalisar Tarayyar Turai da Majalisar Ministoci sun amince da hakan.

Masana sun lura cewa, kamar yadda aka cire Nijeriya daga jerin FATF, wato ƙasashen da aka ayyana a matsayin 'grey-list', haka nan ficewar daga jerin EU na da gagarumin tasiri ga tattalin arziki da harkokin kuɗi.

Kasancewa cikin jerin ƙasashen da ke da haɗari yakan haifar da tsadar gudanar da mu’amaloli, jinkirin biyan kuɗaɗe, taƙaita alaƙar bankuna na ƙasa da ƙasa, da rage jarin waje. An cire Nijeriya daga jerin FATF 'grey-list' a watan Oktoban shekarar da ta gabata bayan aiwatar da jerin gyare-gyare don ƙarfafa tsarin AML/CFT.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa amfani da Tsarin Lura da Kasuwar Canjin Kuɗi ta Zamani (EFEMS), sauya tsarin canjin kuɗi zuwa kasuwa mai ‘yanci, da kuma ƙarfafa kulawa da bankuna, duk suna nuna jajircewar CBN wajen aiwatar da gyare-gyare. Ya ce waɗannan sun ƙarfafa ikon Nijeriya na jure girgizar tattalin arziƙi daga sauyin farashin mai da canjin ra’ayin masu tantance darajar kuɗi.

Ya ce:
“A shekarar 2026, za mu ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, mu ƙarfafa aiki tare da sauran hukumomi da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, tare da bunƙasa sabbin hanyoyin ƙirƙire-ƙirƙire masu ɗaukar alhaki a tsarin kuɗi. Za mu ci gaba da ba da jagora, kare amincin kasuwannin kuɗin mu, amfani da fasahar zamani don inganta yanke shawara, da gina ƙwarewar ma’aikata domin tsarin kuɗi mai ɗorewa.”

Ba da daɗewa ba bayan nada naɗa shi shugabancin CBN, Cardoso ya fara rushe shinge da rashin bayyana gaskiya a tsarin kuɗi da suka jawo saka Nijeriya cikin jerin ƙasashen da EU ta karta wa jan fenti wajen mu'amalar kuɗaɗen.

Daga gyare-gyare a harkokin musayar kuɗaɗe zuwa ƙarfafa sa-ido kan bankunan kasuwanci, CBN ƙarƙashin Cardoso ya yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ficewar Nijeriya daga jerin 'grey-list'.

Daga cikin matakan bin ƙa’idoji akwai tabbatar da cewa bankuna na iya gano ainihin mai mallakar duk wata ma’amala (beneficial owner) tare da tabbatar da sahihancin sa ko akasin haka. Haka kuma, hukumomin kuɗi suna fahimtar tsarin mallaka da iko na abokan hulɗar su, suna sanin manufar dangantakar kasuwanci, tare da ci gaba da sa-ido kan dukkan mu’amaloli a tsawon dangantakar banki.

Shugabar Ƙungiyar Masu Amfani da Bankuna ta Nijeriya (BCAN), Dokta Uju Ogubunka, ta bayyana ficewar Nijeriya daga jerin ƙasashen da EU ke shakkar mu'amalar kuɗaɗe da su cewar wani matsayi ne na samun babban ci gaba.

 Ta yaba wa ƙoƙarin CBN wajen cire ƙasar daga ƙalubalen da ake fuskanta.
Ta ce:
“Wannan zai buɗe sabbin dama ga bankunan Nijeriya da abokan hulɗar su a mu’amala da cibiyoyin kuɗi na ƙasa da ƙasa. Yana nuna cewa tsarin kuɗin Nijeriya amintacce ne ga biyan kuɗaɗe da sauran mu’amaloli. Abin murna ne ga duk ‘yan Nijeriya.”

Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a lokacin da aka cire Najeriya daga jerin FATF 'grey-list', bankin ya ce wannan ya nuna gagarumin ci gaba a tsarin doka, kulawa da aiwatar da hukunci wajen yaƙi da safarar kuɗi, tallafa wa ta’addanci da yaɗuwar makaman hallaka jama’a.

Sanarwar ta lissafo manyan gyare-gyaren da FATF da GIABA suka tantance, ciki har da ƙarfafa kulawa da cibiyoyin kuɗi, faɗaɗa rahoto da sa-ido kan harkokin tura kuɗi, tsarin musayar kuɗaɗen mai tsafta da hada-hadar kuɗaɗe ta zamani wato 'fintech', da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin CBN, NFIU, EFCC da hukumomin tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa ficewar Nijeriya daga jerin 'grey-list' zai rage tsadar bin ƙa’idoji, ya sauƙaƙa samun kuɗin waje, da hanzarta mu’amalolin ƙetare ƙasa, wanda zai taimaka wa kasuwanci, iyalai, da bunƙasar tattalin arziƙi.

Cardoso ya ce kasancewar Nijeriya a jerin ƙasashen da EU ɗora wa karan-tsanar yin hada-hadar kuɗaɗen, ya jawo asarar sama da dala biliyan 30 a jarin da ka iya shigowa ƙasa.

Ya ce, ficewa daga jerin na nuna dawo da amincewar duniya da rage cikas ga bankunan hulɗa.


Rahoton Bankin Duniya na Global Economic Prospects ya ɗaga hasashen bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya a 2026 zuwa kashi 4.4 cikin 100. Rahoton ya ce wannan bunƙasa za ta samu ne sakamakon gyare-gyaren tattalin arziƙi, ingantacciyar manufofin kuɗi, da ƙaruwa a ayyukan hidimomi, noma da masana’antu.


CBN ma ta bayyana cewa shekarar 2026 na ba da dama ta musamman ga daidaita tattalin arziƙi, inda ake sa ran bunƙasa da kashi 4.49 cikin 100 bisa ci gaba da gyare-gyare da sauƙaƙa manufofin kuɗi.

*Ashafa Barkiya ɗan jarida ne mai zaman kan sa, wanda ke nazari kan tattalin arziƙi da matsalolin tsaro.

No comments