Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya buƙaci malaman addinin Musulunci da kafafen yaɗa labarai, tare da kafafen sadarwar zamani da su yi ...
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya buƙaci malaman addinin Musulunci da kafafen yaɗa labarai, tare da kafafen sadarwar zamani da su yi amfani da watan Ramadan mai zuwa a matsayin wata babbar dama ta ƙarfafa zaman lafiya, haƙuri da juna da haɗin kan ƙasa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron Shekara-shekara na shirye-shiryen shiga Ramadan na 2026 da Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a Babban Hedkwatarta da ke Kaduna, wanda ta saba shiryawa a duk shekara.
Gwamna Uba Sani, wanda Sakataran Gwamnatin Jihar Kaduna, Dakta Mu’azu Meyare ya wakilta, ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da zamantakewa da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu sun ƙara ɗora nauyi a wuyan malamai da kafafen yaɗa labarai wajen jagorantar al’umma da hikima, ladabi da tausayi.
Akan hakan, Gwamnan ya yi kira ga malamai da su tabbatar da cewa darussan tafsiri da sauran shirye-shiryen wayar da kai na ramadan suna ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, adalcin zamantakewa da kula da marasa galihu.
Ya bayyana cewa watan ramadan, wata ne mai tsarki da rahama, tarbiyya inda ya buƙaci al’umma da su yi amfani da watan wajen ƙarfafa ɗabi’un sadaka, kishin ƙasa da addu’o’i ga ƙasa da shugabanninta.
Ya ƙara da cewa addu’o’i na gaskiya a wannan wata mai albarka suna da muhimmiyar rawa wajen warkar da ƙasa.
Gwamnan ya kuma yi kira ga gidajen rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta na zamani da su kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa da ladabi wajen watsa tafsiri da sauran shirye-shiryen addini, yana mai gargadin cewa a guji saƙonnin da ka iya tayar da fitina ko rarrabuwar kai.
Ya kumq tunatar da mahalarta cewa yi wa bil’adama hidima na daga cikin manyan ibadu a Musulunci.yana mai bayyana jajircewar Gwamnatin Jihar Kaduna ga shugabanci mai haɗa kowa da kowa, Gwamnan ya ce tsarin haɗin kai tsakanin addinai da gwamnati ta kafa ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabambantan addinai.
Hakazalika, ya tabbatar da goyon bayan gwamnati ga ilimin addini da tattaunawa, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da JNI da sauran ƙungiyoyin addini.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada shirinta na yin aiki kafada da kafada da malamai da kafafen yaɗa labarai domin zurfafa haƙuri, ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da watan Ramadan mai cike da zaman lafiya da albarkar ruhi.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Dakta Abubakar Ibn Umar Garba Abba Kiyari El-Kanemi, wanda ya jagoranci tattaunawar da ta mayar da hankali kan wa’azi mai alhaki, jituwa ta addini da kare zaman lafiya a lokacin Ramadan da bayan sa.
Taron Kafin Ramadan na JNI ya samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da sarakunan gargajiya, fitattun malamai da shugabannin al’umma, lamarin da ya nuna muhimmancin taron a matakin ƙasa wajen tsara tafarkin wa’azi da koyarwar addini gabanin watan Ramadan.







No comments