Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rashin Tsaro Babban Ƙalubale Ne Ga Tattalin Arziki, Za Mu Yi Nasarar Magance Shi — Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta yi nasara kan ta’addanci da ‘yan bindiga, yana mai bayya...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta yi nasara kan ta’addanci da ‘yan bindiga, yana mai bayyana matsalar tsaro a matsayin abin da ba za a amince da shi ba kuma ba daga ɗabi’un al’ummar ƙasar nan ba ne. Shugaban Ƙasar ya ce rashin tsaro ya zama babban ƙalubale ga zaman lafiya da cigaban tattalin arziƙin ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake buɗe taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) karo na biyu da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa. Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar ƙarfafa jami’an tsaro tare da samar da dabarun zamani domin murkushe ayyukan ta’addanci da fashi da makami a faɗin ƙasar.

Shugaban Ƙasar ya jaddada cewa rashin tsaro yana hana bunƙasar tattalin arziƙi, inda ya ce dole ne a haɗa kai tsakanin gwamnati, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar. Ya kuma yabawa gwamnonin jihohin Borno, Katsina da Kaduna bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.

Dangane da tattalin arziƙi, Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau, ciki har da daidaita tattalin arziƙi da dawo da amincewar masu zuba jari. Ya ƙara da cewa jihohi da ƙananan hukumomi yanzu suna samun kaso mafi yawa daga asusun tarayya, lamarin da ke taimaka musu wajen biyan albashi da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Shugaban Ƙasar ya ce Shirin Ci Gaban Ƙasa na Renewed Hope 2026–2030 zai mayar da hankali kan noma, bunƙasa sana’o’i, zuba jari a kiwon dabbobi da kuma ci gaban bil’adama. Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sakamakon taron NEC zai taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa da haɗa kowa a faɗin Nijeriya.
 


No comments