Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya tabbatar da cewa adadin kuɗaɗen waje da ke asusun ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, ya ƙa...
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya tabbatar da cewa adadin kuɗaɗen waje da ke asusun ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, ya ƙaru zuwa dala biliyan 49, abin da ke nuna gagarumin farfaɗowa mai ɗorewa daga kusan dala biliyan 3 gwamnatin nan ta gada a watan Mayun 2023.
Cardoso, ya bayyana cewa kuɗaɗen ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa ya kai dala biliyan 49 ɗin ne tun a ranar 5 ga Fabrairu, 2026, sakamakon ƙaruwa da ya yi daga kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke turowa, fitar da kaya ba na ɗanyen mai ba, da kuma gudummawar ɗaiɗaikun mutane da manyan hukumomi.
Cardoso ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja, yayin karo na biyu na Taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC), wanda ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ya ce wannan ci gaba mai ɗorewa a asusun ajiyar kuɗaɗen waje alama ce bayyananna ta ƙara amincewar jama’a da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ya ce:
“Wannan muhimmin adadi ne ƙwarai. A lokacin da muka karɓi aiki, asusun ajiyar kuɗaɗen waje bai wuce dala biliyan 3 ba. Zuwa ƙarshen shekarar da ta gabata, ya ƙaru sosai zuwa sama da dala biliyan 30. Kuma kamar yadda na faɗa, zuwa 5 ga Fabrairu, 2026, ya kai dala biliyan 49. Yanzu mu ne masu sayen kuɗin waje."
Ya bayyana cewa yanzu CBN na barin kasuwar musayar kuɗi ta ƙayyade farashi gaba ɗaya, yayin da bankin ke shiga tsakani ne kawai domin sayen kuɗin waje idan buƙata ta taso.
A cewar sa, wannan tsari ya taimaka wajen rage bambanci tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan-fage.
Ya ce:
“Bambancin da ke tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan-fage ya ragu zuwa ƙasa da kashi biyu cikin ɗari.”
Ya jaddada cewa kuɗaɗen da ‘yan Njeriya mazauna ƙasashen waje ke turowa gida sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan adadin asusun ajiyar kuɗaɗen waje.
Ya ce ‘yan Nijeriya a ƙetare sun fito daga dukkan jihohin ƙasar kuma suna da sha’awar tallafa wa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar turo kuɗi gida.
Ya ce:
“Kuɗaɗen da ‘yan ƙetare ke turowa sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa asusun ajiyar mu. Sun fito daga kowace jiha da ke faɗin ƙasar nan. Muna yi hulɗa da su kuma mun sauƙaƙa musu hanyoyin tura kuɗi zuwa gida.”
Ya ƙara da cewa haɗin kai daga gwamnonin jihohi da sauran shugabanni zai kasance muhimmi wajen ɗorewar wannan ci gaba a shekarun da ke tafe.
Cardoso ya ce sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sun sa samun kuɗin waje ya zama mafi sauƙi ga ‘yan ƙasa, musamman masu tafiya ƙasashen waje.
Ya ce:
“Yanzu idan mutum zai yi tafiya, ba sai ya nemi kuɗin waje ba. Kana amfani da katin nairar ka ka biya duk abin da ka ke so. Yanzu naira ta fi gasa, kuma mutane ba sa tsoron riƙe naira.”
Ya tuna cewa a baya ana ƙin karɓar naira a wasu ƙasashen yankin Yammacin Afirka, amma ya ce wannan ya zama tarihi.
Ya ce:
“A wancan lokacin, idan ka kai naira wasu ƙasashen Yammacin Afirka, ba wanda ke son karɓa. Yanzu wannan ya wuce. Akwai tabbas, kuma mutum zai iya yin shiri.”
Ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da ke ajiye kuɗin waje ba tare da wata buƙata ta gaskiya ba cewa hakan na iya jawo musu asara.
Game da ɓangaren bankuna, Cardoso ya ce ana ci gaba da ƙara ƙarfafa jarin bankuna domin ƙarfafa su da kuma shirya su don tallafa wa manyan manufofin tattalin arziƙin ƙasa, ciki har da burin gina tattalin arziƙin da zai kai dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2026.
Ya ce:
“Mun san muhimmancin tsarin banki. Bankuna suna ƙara jari, masu zuba jari suna samun riba ta gaske, kuma kasuwar hannun jari na farfaɗowa sakamakon ingantattun kuɗaɗen shiga da kwanciyar hankali.”
Ya ƙara da cewa CBN na aiki kan ƙa’idojin maye gurbin shugabanci a bankuna domin tabbatar da sauyin shugabanci cikin sauƙi da kuma ƙarfafa juriyar bankuna a lokutan ƙalubale.
Cardoso ya ce sabbin bayanan tattalin arziƙi na nuna alamun kwanciyar hankali, inda ya nuna haɓakar ƙarfin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.98 cikin ɗari, matsayi mai ƙarfi na asusun kasuwanci na ƙasa, da kuma rarar dala biliyan 3.42 da aka samu a zango na uku na shekarar 2025.

No comments