Wani mummunan al’amari ya girgiza al’ummar Jihar Yobe bayan rasuwar wani ɗalibi mai shekaru 17, Hassan Ahmadu, ɗalibin aji na uku na babbar ...
Wani mummunan al’amari ya girgiza al’ummar Jihar Yobe bayan rasuwar wani ɗalibi mai shekaru 17, Hassan Ahmadu, ɗalibin aji na uku na babbar sakandare (SS3) a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnati da ke Potiskum.
Lamarin, wanda ya faru ranar Lahadi a harabar makarantar da ke ƙaramar hukumar Potiskum, ya bar ɗalibai da malamai cikin jimami da ruɗani.
Rahotanni sun nuna cewa an ce Hassan ya rasu ne sakamakon wani hari da wasu abokan karatun sa suka kai masa, lamarin da ake zargin yana da alaƙa da cin zarafi da aka daɗe ana yi masa.
Wata majiya daga cikin iyalan sa ta bayyana cewa an yi jana’izar sa a ranar da lamarin ya faru, a garin su na Gadaka, ƙaramar hukumar Fika, inda aka binne shi cikin alhini da hawaye.
Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan abin da ya haddasa rasuwar tasa ba. Sai dai an tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma ɗaukar matakan da suka dace.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara bincike domin tantance musabbabin mutuwar ɗalibin. A cewarsa, “Mun samu labarin abin da ya faru, kuma bincike yana gudana don gano dalilan da suka kai ga mutuwar dalibin.”
Wani malami a makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce an daɗe ana cin zarafin Hassan daga wasu abokan karatun sa. Ya bayyana cewa a ranar Lahadi ne Hassan ya nemi su daina muzgunawa da tsangwama masa, amma lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali. “Sun buge shi sosai, daga baya kuma ya rasu. Abin ya girgiza makarantar baki ɗaya,” inji malamin.
Bayan aukuwar lamarin, hukumomin makarantar sun miƙa waɗanda ake zargi ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike. Malamin ya ƙara da cewa makarantar na fatan hukumomi za su gudanar da bincike mai zurfi tare da tabbatar da an ɗauki matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.
Lokacin da aka tuntubi Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Yobe, Farfesa Abba Idriss Adam, ya ce zai dawo da cikakken bayani bayan ya samu sahihan rahotanni kan abin da ya faru.
Lamarin ya sake tayar da hankalin jama’a kan matsalar cin zali a makarantu, wadda masana ke ganin na iya haifar da mummunan sakamako idan ba a sauki matakan kariya da wayar da kai ba. Yanzu dai iyaye da malamai na kira ga a ƙara tsaurara matakan sa ido da kulawa domin tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar ɗalibai a makarantu.

No comments