Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JNI Ta Gargaɗi Malamai Kan Bin Ƙa’idojin Tafsiri, Ta Nuna Damuwa Kan Tsaro Da Tattalin Arziki

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta buƙaci malamai da masu gabatar da Tafsirin Alqur'ani Mai Girma a watan Ramadan da su tsare amana...

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta buƙaci malamai da masu gabatar da Tafsirin Alqur'ani Mai Girma a watan Ramadan da su tsare amanar da aka ɗora musu ta hanyar bin Alƙur’ani da Sunnah cikin tsari da daidaito, domin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da tarbiyya a tsakanin al’umma.

Wannan kira ya fito ne a taron shekara-shekara na tunkarar watan Ramadan da aka gudanar a Kaduna, inda Sakatare-Janar na JNI, Farfesa Khalid Aliyu, ya gabatar da rahoto kan yadda aka gudanar da Tafsirin Ramadan na 2025.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Mataimakin Shugaban JNI kuma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi; da sarakuna, malamai da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasa.

A cikin jawabin nasa, Farfesa Aliyu ya bayyana Tafsiri a matsayin wata amana mai tsarki wadda ke buƙatar tsantseni da hikima.

Ya gargaɗi malamai da su guji furta kalamai masu tayar da hankali, tsokanar mazhabobi, kai hari ga juna ko amfani da nassosin Alƙur’ani don biyan buƙatun kai ko na aƙida.

A cewarsa, sa ido da JNI ta yi kan Tafsirin Ramadan na bara ya nuna cewa duk da yawancin malamai sun bi ƙa’idoji, akwai waɗanda suka kauce, abin da ke buƙatar ƙarin kulawa da jan hankali.

JNI ta jaddada cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen jan kunnen duk malamin da aka samu ya saɓa ƙa’idojin Tafsiri, tare da miƙa batun ga sarakuna da hukumomin da suka dace idan buƙatar hakan ta taso.

Ƙungiyar ta yaba da yadda malamai ke kai wa juna ziyara a wuraren Tafsiri a cikin al’umma ɗaya, tana mai cewa hakan alama ce ta ƙarfafa zumunci da kawar da saɓani.

Haka kuma ta buƙaci a ƙara maida hankali kan wa’azi game da shaye-shaye, rashin ɗa’a da tashin hankalin matasa, tana mai cewa matsalar shan miyagun ƙwayoyi ta zama babbar barazana ga zamantakewar al’umma.

Dangane da al’amuran ƙasa, JNI ta nuna damuwa kan ci gaba da matsalolin tsaro, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakai masu ƙarfi kan ’yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci.

Ta kuma yi Allah-wadai da kashe-kashen da suka auku a Kaiama, tana kira da a guji ɗora matsalolin tsaro kan wata ɓangare guda ta hanyar rahotanni masu nuna wariya.

Game da batun zargin sacewa da cin zarafin wata budurwa, Walida Abdullahi, JNI ta buƙaci a gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi ba tare da son rai ba.

Ƙungiyar ta kuma bayyana damuwarta kan sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurka ta ayyana a matsayin “Ƙasashe Masu Damuwa”, tana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen warware matsalar.

A ƙarshe, JNI ta jaddada muhimmancin farfaɗo da tsarin Zakka da Waqafi tare da haɗin gwiwar AZAWON domin rage talauci, tana mai kira ga masarautu su sake rungumar wannan tsari. 

Taron ya ƙare da kira ga Musulmi da su yi amfani da watan Ramadan wajen gyaran zuciya, ƙara ibada da kuma yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.





 

No comments