Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sanusi-Mika’ilu, ya nuna matuƙar damuwa kan abin da ya kira “azaba biyu” da masu amfani da wutar lantarki ke fu...
Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sanusi-Mika’ilu, ya nuna matuƙar damuwa kan abin da ya kira “azaba biyu” da masu amfani da wutar lantarki ke fuskanta a Nijeriya, inda ya ce ba adalci ba ne a tilasta wa al’umma sayen na’urorin lantark, kamar taransifoma, sannan a sake ɗora musu cikakken biyan kuɗin wuta ba tare da rangwame ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Zuru a ranar Litinin yayin da ya karbi baƙuncin shugabannin Kebbi Development Forum (KDF) a ziyarar girmamawa da suka kai masa a ƙarƙashin Kebbi Electricity Forum (KEF).
Ya ce, abin takaici ne yadda idan taransifoma, sandar wuta ko wata na’ura ta lalace, al’umma ne ke tara kuɗaɗe su sayo sabuwa, amma da zarar an saka, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KEDCO) zai fara karvar kuɗin wuta nan take ba tare da la’akari da irin nauyin da jama’a suka ɗauka ba.
A cewarsa, a wasu lokutan ma al’umma kan nemi taimakon ‘yan siyasa domin samar da irin waɗannan kayayyaki, amma duk da haka sai su sake biyan KEDCO kuɗin sakawa, sannan a fara musu lissafin biyan wuta kamar yadda aka saba.
Sarkin ya bayyana cewa a irin wannan yanayi, ya dace kamfanin ya samar da wata hanya ta mayar wa al’umma da kuɗin da suka kashe, ta hanyar dakatar da karbar kudin wuta na wani lokaci har sai an biya cikakken kuɗin kayan da suka saya.
“Ya kamata a biya musu kashi 100 cikin 100 na kuɗin da suka kashe kafin a fara karbar kuɗin wuta daga gare su,” inji shi.
Ya kuma yi alƙawarin kafa kwamitin wutar lantarki a masarautar Zuru domin samar da cikakken tsarin doka da zai riƙa bibiyar duk wani mataki da ya shafi dawo da wutar lantarki da kuma kare muradun jama’a.
Sarkin ya jaddada cewa wutar lantarki ginshiƙi ce na ci gaba, yana mai cewa ba za a iya cimma wani gagarumin ci gaba ba tare da wadatacciyar wuta ba.
Tun da farko, Shugaban Kebbi Development Forum, Alhaji Usman Abubakar, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin tattaunawa da al’umma da kuma faɗakar da su kan yadda ake amfani da wuta yadda ya kamata, tare da muhimmancin biyan kuɗin wuta a kan lokaci.
Ya ce akwai tsari da dokoki da ake bi wajen neman a mayar wa al’umma da kuɗin da suka kashe wajen sayen taransifoma ko wasu kayayyaki, don haka ya jaddada buƙatar wayar da kan jama’a domin su san haƙƙoƙinsu da abin da ya rataya a wuyansu.
Abubakar ya ƙara da cewa, a haɗin gwiwa da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), za su zagaya dukkan masarautu huɗu na jihar domin ilimantar da jama’a kan haƙƙoƙinsu da kuma kare kayayyakin lantarki daga varna.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi kan tallafin Naira miliyan 650 da ta bai wa KEDCO domin sayen taransifoma mai ƙarfin 15MVA, da kuma tallafin Naira miliyan 150 da take bayarwa duk wata don ƙara inganta samar da wuta a faɗin jihar.
A ƙarshe, ya buƙaci al’umma da su ɗauki kayayyakin lantarki a matsayin nasu, su kare su daga barna, tare da tabbatar da biyan kuɗin wuta kan lokaci domin ɗorewar samar da wutar lantarki.
.jpg)
No comments