Fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Aisha Yesufu, ta yi zazzafar muhawara da jami’an ’yan sanda a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙa...
Fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Aisha Yesufu, ta yi zazzafar muhawara da jami’an ’yan sanda a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa yayin zanga-zangar neman gyaran dokar zabe a Abuja.
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda Yesufu ke magana kai tsaye da jami’an tsaro, tana sukar abin da ta kira nuna ƙarfin iko kan talakawa, alhali matsalar tsaro na ci gaba da hallaka rayukan ’yan ƙasa a sassa daban-daban na Nijeriya.
Ta ce, abin takaici ne yadda ake tura jami’an tsaro domin kare shugabanni, alhali talakawa na fuskantar hare-hare da kashe-kashe a kullum. A cewarta, shugabannin da ake bai wa kariya ba za su tsaya wa jami’an tsaron ba idan lokaci ya ƙure.
“Yara ana kashe su a ƙasar nan, amma ku na tsaron waɗanda ba za su tsaya muku ba. Bayan kun yi ritaya, ku ma za ku dawo cikin waɗannan mutane,” inji ta.
A wani bangare na jawabin nata da ya ɗauki hankalin masu zanga-zanga da masu kallo, Yesufu ta tambayi jami’an ko ba su jin kunyar tsoratar da fararen hula masu neman haƙƙinsu ba. Ta ce mafi muni da za su iya yi mata shi ne duka ko harbe ta, tana mai nuna cewa ba za ta ja da baya ba.
Zanga-zangar dai na da nasaba da matakin Majalisar Dattawa na kin amincewa da sanya tilas watsa sakamakon zabe ta hanyar lantarki kai tsaye, a karkashin gyaran dokar zabe. Masu zanga-zangar na neman a tilasta watsa sakamako kai tsaye domin kauce wa zargin magudi da rashin gaskiya a zabuka masu zuwa.
An gudanar da zanga-zangar ne karkashin taken “Occupy National Assembly”, inda ƙungiyoyin fararen hula da ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa suka halarta. Tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ma ya halarci zanga-zangar tare da dansa, yana mai sukar matakin da ya ce zai iya jefa shakku a kan sahihancin zabuka masu zuwa.
A nata bangaren, Majalisar Dattawa ta bayyana cewa ba ta soke watsa sakamakon zabe ta lantarki gaba daya ba, sai dai ta cire kalmar “kai tsaye” domin bai wa Hukumar Zabe ta Kasa ’yancin tsara hanyar da ta dace bisa la’akari da kalubalen sadarwa da tsaro.
Sai dai matakin ya jawo muhawara mai zafi a fadin kasa, inda bangarori da dama ke ganin wajibi ne a fayyace dokar domin kar a samu sabani a aiwatar da ita.

No comments