Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewa yana tafiyar da wani gungu a cikin gwamnatinsa, yana mai cewa wannan tsarin ne ke taimaka m...
Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewa yana tafiyar da wani gungu a cikin gwamnatinsa, yana mai cewa wannan tsarin ne ke taimaka masa wajen samun nasara a ayyukan da yake aiwatarwa.
Ododo ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga jama’a a wajen ƙaddamar da wani aiki a jihar, inda ya ce ba ya boye gaskiyar cewa yana da wadanda da ke taimaka masa wajen yanke shawara da aiwatar da manufofi.
Ododo ya ƙara da cewa, sabanin yadda ake kallon samar da makusanta a siyasar Nijeriya a matsayin wata kungiya mai illa, nasa suna aiki ne yadda ya kamata
Gwamnan ya bayyana cewa shi ma a baya ya taba zama cikin wani gungu a karkashin tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
A cewarsa, “Ni ma na taba zama cikin cabal, amma namu a wancan lokacin ba su iya aiki kamar yadda wannan yake aiki a yanzu ba.”
Ya ce wannan ne ya sa yake jaddada cewa ba samar da gungun masu fada a ji ne matsala ba, illa yadda ake tafiyar da shi da irin rawar da suke takawa a mulki.
Ododo ya bayyana sunan shugabar makusantansa cewa ita ce Hajiya Dr. Habibat Tijani Aliyu, babbar akantar jihar, yana mai cewa tsohon gwamna Yahaya Bello ne ya amince da naɗinta.
Ya ce, “Shugabar makusanta na, wadda Mai Girma Alhaji Yahaya Bello ya amince da ita, ita ce Hajia Dr. Habibat Tijani Aliyu.”
Gwamnan ya ce, babban mai binciken kuɗi na jihar na cikinsu, haka nan shugaban jam’iyya, da kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarauta duk na cikin makusatan sa.
Ododo ya ce, nasarar mulki na rataye ne a kan yadda kungiyoyin da ke kusa da shugaba ke aiki.
Ya ce idan makusantan gwamna za su taimaka wajen tafiyar da gwamnati cikin tsari da gaskiya, to babu laifi a samu irin hakan.
Ododo ya zama gwamna ne bayan ya taba riƙe mukamin babban mai binciken kuɗi na kananan hukumomi a zamanin Yahaya Bello, wanda ya mulki Kogi daga 2016 zuwa 2024.

No comments