Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnati Ta Yi Ƙarin Haske Game Da Harin Haɗin Gwiwar Amurka A Kan ISIS A Jihar Sokoto Da Kwara

Ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kai ta bayyana cewa Gwamnatin Nijeriya ta na sanar da nasarar kai hare-haren da aka tsara cikin tsan...


Ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kai ta bayyana cewa Gwamnatin Nijeriya ta na sanar da nasarar kai hare-haren da aka tsara cikin tsanaki kan wasu manyan sansanonin ’yan ta’addan ISIS guda biyu da ke cikin dajin Bauni, a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.

A wata sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fitar, ta bayyana cewa an gudanar da harin ne tare da haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Ƙasar Amurka, bayan bayanan sirri sun tabbatar da cewa ’yan ISIS daga yankin Sahel na amfani da wuraren a matsayin wajen taro da shiryawa domin kai manyan hare-haren ta’addanci a cikin ƙasar nan, tare da taimakon wasu ƙungiyoyin ta’addanci na cikin gida.

Sanarwar ta ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 12:12 na dare zuwa 1:30 na safiyar Juma’a, 26 ga Disamba, 2025, bayan samun cikakken amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

An bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ƙarƙashin tsayayyen tsarin umarni da jagoranci, tare da shigar Rundunar Sojin Nijeriya, a ƙarƙashin kulawar Ministan Tsaro, Ministan Harkokin Waje, da Babban Hafsan Tsaro.

Hare-haren sun samo asali ne daga tashar jiragen ruwa da ke yankin Tekun Guinea, bayan dogon nazarin bayanan sirri, shirye-shiryen aiki da bincike na sama. Jimillar harsasai masu bin tsarin GPS guda 16 ne aka yi amfani da su ta hanyar jiragen sama marasa matuƙa samfurin MQ-9 Reaper, lamarin da ya kai ga kawar da ’yan ISIS ɗin da ke ƙoƙarin shigowa Nijeriya ta hanyar yankin Sahel.

Sai dai a yayin aikin, wasu ragowar harsasai sun faɗo a yankin Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sokoto, da kuma a Offa ta Jihar Kwara, kusa da wani otel. Gwamnati ta tabbatar da cewa babu wani farar hula da ya jikkata a wuraren, kuma jami’an tsaro sun gaggauta killace yankunan.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kawar da duk wata barazanar ta’addanci, musamman daga ƙungiyoyin ta’addanci na ƙetare da ke ƙoƙarin tauye ikon Nijeriya da tsaron al’ummarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa Nijeriya na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙawayenta na dabarun tsaro da abokan hulɗa domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, tsaron iyakoki da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamnati ta tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa tana da cikakken iko kan tsarin tsaron ƙasa, tare da ƙudirin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. An kuma buƙaci al’umma da su kasance cikin kwanciyar hankali da taka-tsantsan yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe duk wata ƙungiyar ta’addanci da ke barazana ga ƙasa.
 

No comments