Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, tare da ceto mutane 34 da aka sace, a jerin ...
Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, tare da ceto mutane 34 da aka sace, a jerin hare-haren haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga Disamba, 2025.
Wata majiya mai tushe daga Hedkwatar Sojin Ƙasa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa an samu waɗannan nasarori ne a jihohin Borno, Adamawa, Sokoto, Katsina, Neja, Zamfara, Filato, Delta, Cross River da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
A jihar Borno, majiyar ta ce hare-haren sama tare da bin diddigi na ƙasa da aka kai a Sowolwolo, cikin Ƙaramar Hukumar Bama, da kewayenta, sun yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda 19, tare da rusa sansanonin ajiyar kayayyakin su da tarwatsa hanyoyin sadarwar ISWAP da JAS.
Ta ƙara da cewa wasu hare-hare na gaba da aka kai a yankunan Gulumba Gana, Kumshe, Kasho Miri da Chongolokura sun yi sanadin hallaka ƙarin ‘yan ta’adda 38. Haka kuma, bayanan leƙen asiri da sa ido (ISR) sun gano manyan shugabannin ‘yan ta’adda da ake shirin kai musu hari nan gaba.
A jihohin Neja da Katsina kuwa, majiyar ta bayyana cewa dakarun soji sun fatattaki hare-haren ‘yan ta’adda da aka kai sansanin FOB Kwanar Dutse a Ƙaramar Hukumar Mariga, da kuma kan hanyar Shanono–Katsina. A yayin wannan samame, an ceto farar hula guda ɗaya tare da ƙwato shanu 78 da tumaki 28 da ‘yan ta’addan suka sace.
Game da ayyukan ceto daga hannun masu garkuwa da mutane, majiyar ta ce a jihar Kebbi, dakarun Bataliya ta 223 sun ceto mutane 16 bayan samun bayanan sirri a ƙauyen Unashi da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu.
A jihar Filato kuma, an ceto mutum guda a yankin Yaka Naji Jandutse da ke Ƙaramar Hukumar Wase.
Majiyar ta ƙara da cewa dakarun sun kuma dakile ayyukan ta’addanci da laifuka a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka cafke masu haƙar ma’adinan zinare ba bisa ƙa’ida ba guda 11 a birnin Tarayya Abuja. Haka kuma, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami a Filato, tare da kwato kuɗaɗen da suka sace.
A jihar Delta, an cafke masu satar ɗanyen mai guda biyu, inda aka ƙwato jarkoki 104 (lita 2,600) na ɗanyen mai. A Cross River kuwa, an kama wasu da ake zargin ‘yan fashin teku nr mutum uku da ke da alaƙa da ƙungiyar ‘yan bindiga ta BIG JOE.
Majiyar ta jaddada cewa waɗannan ayyuka na nuna ƙudirin sojojin Nijeriya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tabbatar da bin doka da oda, da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankunan da abin ya shafa.
Ta kuma sake tabbatar da aniyar Rundunar Sojin Ƙasa ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri, ceto waɗanda aka sace, da kuma murƙushe duk wata barazana daga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

No comments