Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Ƙudirin Bin Doka Da Oda, Kuma Ta Yi Watsi Da Zargin Kai Wa 'Yan Adawa Hari

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na kamawa ko tsare ko gurfanar da ’yan adawa ba bisa ƙa’ida ba.  Ministan Yaɗa Labarai...

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na kamawa ko tsare ko gurfanar da ’yan adawa ba bisa ƙa’ida ba. 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Talata sakamakon ɓullar wata takardar bogi da ke yawo wadda ke zargin wai an kafa wata rundunar haɗin gwiwa domin wani shiri da aka yi wa laƙabi da “ADP4VIP” (Arrest, Detain, Prosecute for Very Important Persons" – wato Kamawa, Tsarewa da Gurfanar da Manyan Mutane).

Ministan ya ce: "Wannan takarda marar tushe ta yi ƙaryar cewa wai an kafa wata runduna da ta ƙunshi haɗakar hukumomin EFCC da ICPC da Sashen Bayanan Kuɗi na Nijeriya (NFIU), kuma wai Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Ƙasa ne yake jagorantar haɗakar domin kai farmaki ga fitattun ’yan adawa ba tare da bin ƙa’ida ba.

"Waɗanda suka ƙirƙiri wannan labarin ƙaryar sun yi iƙirarin wai 'majiyoyi masu tushe da dama' ne suka shaida musu hakan domin kawai su ƙallafa zargin cewa ana shirin 'raunana da murƙushe harkokin siyasar ’yan adawa da gangan,' musamman 'yan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC)."

Idris ya jaddada matsayin Gwamnatin Tarayya da cewa, "Babu wani shiri mai suna 'ADP4VIP' domin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana mai da hankali sosai kuma cikin nasara kan muhimman manufofin ta da suka haɗa da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki masu kyakkyawan sakamako, yaƙi da matsalar tsaro, faɗaɗa damar kasuwanci, da dawo da amincewar masu zuba jari.

"Ƙoƙarin da wasu ’yan adawa suke yi na fassara bin doka da ladabtarwa a matsayin tsangwamar 'yan siyasa, dabara ce mai haɗari da aka tsara domin kare wasu da ake kira manyan mutane daga fuskantar dokokin ƙasa da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa."

Ya ƙara da cewa gwamnati ta jaddada ginshiƙan manufofin ta na asali, inda ya yi nuni da cewa Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka yi wa gyara) ya ba kowane ɗan Nijeriya 'yanci na haɗuwa da taruwa ba tare da tsangwama ba. 

"Shugaba Tinubu ya yi rantsuwar kare wannan Kundin Tsarin Mulki da tanade-tanaden sa, ciki har da ’yancin haɗuwa da kuma ’yancin addini. 

"Shi cikakken mai bin tafarkin dimokiraɗiyya ne wanda ke da tarihin ayyuka nagari kuma tabbatattu.

"A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, Gwamnatin Tarayya tana nan daram kan girmama doka, bin ƙa’ida, da tabbatar da ’yancin aiki na hukumomi. 

"Nijeriya ƙasa ce ta dimokiraɗiyyar kundin tsarin mulki, inda hukumomin tsaro da na shari’a suke da alhakin gudanar da ayyukan su cikin ƙwarewa, ba tare da ana tsoma musu baki a aikin su ba, kuma don amfanin ƙasa."

Ministan ya yi kira ga ’yan siyasa da sauran jama'ar ƙasa da su guji yaɗa labaran ƙarya ko ruɗani da labaran bogi, musamman a wannan zamani da daraja da sahihanci ke da alaƙa kai-tsaye da ingancin labarai.

Ya ce: "Yayin da ake ƙara kusantar manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2027, ya kamata jama’a su sa ran za a samu ƙaruwar labaran ƙarya da cin zarafin 'yan siyasa daga wasu da suke amfani da ƙarya a matsayin makamin neman suna da dauƙaƙa.

"Muna roƙon dukkan ’yan Nijeriya da su kasance masu lura, tare da ƙin amincewa da siyasar karkatar da gaskiya da rarrabuwar kai.

"Kowane ɗan Nijeriya yana da ’yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na yin harkokin sa na siyasa da yin hulɗa a bisa doka. A lokaci guda kuma, hukumomin tsaro da na yaƙi da cin hanci da rashawa suna da cikakken iko da doka ta ba su na yi aiki don amfanin ƙasa.

"Yayin da muke rufe shafin shekarar 2025 tare da shiga sabuwar shekara, wannan gwamnati ba za ta bari a shagaltar da ita da siyasar banza ba. ’Yan Nijeriya sun cancanci su samu cigaba mai ɗorewa, bunƙasa da sakamako a fili—kuma wannan shi ne abin da Gwamnatin Tinubu ta jajirce wajen samarwa."
 

No comments