Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Saɓani Ya Ɓarke Tsakanin Sojoji Da ’Yan Sanda Kan Kama Ɗan Ƙunar Baƙin Wake A Borno

Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta ƙaryata rahotannin da ke cewa sojojin Nijeriya ne suka kama wani da ake zargin mai shirin kai harin ƙuna...



Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta ƙaryata rahotannin da ke cewa sojojin Nijeriya ne suka kama wani da ake zargin mai shirin kai harin ƙunar baƙin wake a jihar, tana mai jaddada cewa ita ce ta gudanar da aikin kama mutumin, kuma babu wata na’urar fashewa mai aiki da aka samu a tare da shi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Borno, ASP Nahum Daso, ya bayyana rahotannin a matsayin kuskure da ke yaudarar jama’a, yana mai cewa bayanan da sojoji suka fitar ba su yi daidai da gaskiyar abin da ya faru ba.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton da kafafen yaɗa labarai suka wallafa a daren Talata, wanda ya danganta kama wani da ake zargi ɗan ƙunar baƙin wake ga dakarun Operation Hadin Kai.

A cewar sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, dakarun rundunar sun kama mutumin mai suna Abubakar Mustapha a yankin Banki, cikin ƙaramar hukumar Bama.

Sanarwar ta sojoji ta yi iƙirarin cewa an kama wanda ake zargin ne da wasu kayan da ake zaton sassan na’urar fashewa ce, lamarin da ya nuna yiwuwar shirin kai hari cikin gaggawa. Ta ce kama mutumin ya biyo bayan bayanan sirri da kuma ci gaba da ayyukan haɗin gwiwa domin tabbatar da tsaron yankin Banki.

Sai dai rundunar ’yan sanda ta ce wannan bayani bai dace da abin da ya faru ba. A cewarta, jami’anta ne suka kama mutumin, kuma binciken farko bai gano wata na’urar fashewa mai aiki ba. 

Rundunar ta ce duk da ana ci gaba da bincike, ya zama wajibi a rika fitar da sahihin bayani domin kauce wa tayar da hankalin jama’a.

Batun ya sake bayyana matsalar rikice-rikicen bayanai tsakanin hukumomin tsaro a yankin Arewa maso Gabas, inda sau da dama ake samun saɓani kan yadda ake bayyana nasarorin tsaro. Masana tsaro na ganin irin wannan yanayi na iya rage amincewar jama’a da bayanan hukumomi, musamman a jihohin da ke fama da barazanar ta’addanci.

Rundunar ’yan sandan Borno ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tana mai cewa tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

No comments