Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jam'iyyar APC A Zamfara Ta Ƙaddamar Da Horar Da Jami'an Da Za Su Yi wa Mambobin Ta Rijista

Daga Hussaini Yero, Gusau  Jami'yyar APC A Jihar Zamfara,ta ƙaddamar da horar da jami'an da za su gudanar da Rijistar 'yan Jami...


Daga Hussaini Yero, Gusau 

Jami'yyar APC A Jihar Zamfara,ta ƙaddamar da horar da jami'an da za su gudanar da Rijistar 'yan Jami'yyar a faɗin Jihar Zamfara.

Shugaban shirin na jiha, shi ne jami'in yaɗa labarai na Jami'yyar na Jiha, Malam Yusuf Idris Gusau.

A wani taro da suka kira, Malam Yusuf ya bayyana cewa ,Uwar Jami'yyar APC ta ƙasa ce ta bullo da wannnan Shirin sabunta Rijista da duk ɗan Jami'yyar, don haka duk wanda bai sabunta tashi Rijista ba ,lallai ba zai zamo memba na Jami'yyar ba.

Alhaji Yusif Idris ya bayan cewa horon, wanda ya ƙunshi kimanin wakilan jam'iyyar APC (Agents) su 294 daga mazabu 147, inda wakilai biyu-biyu ke wakiltar kowace mazauna, da kuma jami'an sa ido (Supervisors) su 14 inda mutum ɗaya-ɗaya ke wakiltar kowace karamar hukuma ya soma ne da yankin zamfara tsakkiya da ya kunshi kananan hukumomin Gusau, Tsafe, Maru da kuma Bungudu.

A ƙarƙashin shirin, kowane yanki (Zobe) na ƙarƙashin jami'in jam'iyya da ake kira "Kodineta' da zai kula da aikin a yankin da aka ɗora masa, inda yankin zamfara ta tsakkiya ke ƙarƙashin kulawar mataimakin sakataren tsare-tsare jam'iyyar APC na jiha, Hon Bello Mai Jama'a Tsafe. Sai yankin zamfara ta Arewa da ke ƙarƙashin Hon. Muhammad Nasiru Albashir Ƙaura.

Sai yankin zamfara ta yamma zai kasance ƙarƙashin kulawar mai baiwa jam'iyyar APC shawara ta fuskar shari'a, Barrister Aliyu Muhammad Bukkuyu, yayin da shirin a matakin jiha kachokan ke ƙarƙashin jagorancin sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC ta jiha,Yusuf Idris Gusau.

Ƙarƙashin tsarin Rijistar za a bayar da na'urorin masu aiki da ƙwaƙwalwa ga jami'an da za su gudanar da shirin inda aka bayyana cewa duk jami'an da ya baro mazabar sa zuwa wata mazaba to na'urar ba za ya yi aiki ba domin ya fita daga "Kodineta" kasancewa an tsara ma ta komai.

Rijistar ƴaƴan jam'iyya na karkashin umurni da tsare tsare uwar jam'iyyar APC ta ƙasa domin sabunta rijistar ƴayan ta a duk fadin tarayya Nijeriya domin tabbatar da ƴaƴan ya ma su ladabi da biyayya kadai su ka saka mallaki wannan rijista.

 Mallakar rijistar jam'iyya sharadi ne ga duk dan jam'iyyar APC da ke sha'awar yin takara kujerarin shugabancin jam'iyya da sauran kujerin wakilcin al'umma wanda rashin sa na kore ma dan jam'iyya hakkin shiga zabe ko a zabe shi.

Kodinetan yayi godiya ga Sanata Abdul'aziz Yari Marafan Sokoto da Minista Matawalle Maradun aka kokarin da sukeyi na cigaban Jamiyyar.
 

No comments