Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

HARIN SAKKWATO: Ba Mu Taɓa Bai Wa ’Yan Ta’adda Ko ’Yan Bindiga Mafaka Ba – Sarkin Jabo

Sarkin Fawan Jabo, Muhammadu Abubakar, ya jaddada cewa al’ummomin Jabo da Bargini da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato ba su taɓa...



Sarkin Fawan Jabo, Muhammadu Abubakar, ya jaddada cewa al’ummomin Jabo da Bargini da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato ba su taɓa zama mafakar ’yan ta’adda ko ’yan bindiga ba, yana mai bayyana yankin a matsayin wuri mai cike da zaman lafiya tun shekaru masu yawa da suka wuce.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan abin da ya faru a daren Laraba, lokacin da wani abu mai fashewa daga sararin samaniya ya sauka, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da ruɗani.

A cewarsa, mutanen yankin sun daɗe suna rayuwa cikin kwanciyar hankali ba tare da tarihin aikata laifukan ta’addanci ko garkuwa da mutane ba.

“Ba mu taɓa bai wa ’yan ta’adda ko ’yan bindiga mafaka a cikin wannan yanki ba. Wannan wuri ya daɗe yana cikin salama, kuma wannan ne ya sa abin da ya faru ya tayar mana da hankali matuƙa,” in ji sarkin.

Sarkin ya ƙara da cewa, abin da ya fi kamanceceniya da barazanar tsaro a yankin ya faru ne kusan shekaru fiye da ashirin da suka wuce, inda aka samu rahoton sace mutum guda a shekarar 2000, amma tun daga wannan lokaci yankin ya ci gaba da kasancewa lafiya.

Ya ce lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na dare, ƙarar da aka ji da kuma yadda abin ya faɗo cikin hanzari ya sa mutane da dama suka yi zaton hatsarin jirgin sama ne. Sarkin ya bayyana cewa jama’a sun firgita matuƙa, wasu na gudu suna neman mafaka domin tsira da rayukansu.

Sai dai daga baya, bayan mutane sun sami ƙarfin gwiwar kusantar wurin, aka gano cewa ba jirgin sama ba ne, amma wani abu daban da ya faɗo tare da wuta da hayaki mai yawa.

Sarkin Fawan Jabo ya yi kira ga hukumomi da su yi cikakken bincike kan lamarin, domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru, tare da kare mutuncin al’ummomin yankin daga duk wata zargi da ba su dace ba. Ya ce al’ummar Jabo da Bargini mutane ne masu son zaman lafiya, kuma za su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da dorewar tsaro a yankinsu.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya kare yankin daga duk wani abin tashin hankali a nan gaba, tare da fatan al’umma za su ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar yadda suka saba tsawon shekaru.

No comments