Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka ɗauka a matsayin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a jihohi bakwai...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka ɗauka a matsayin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a jihohi bakwai da ake ganin suna fuskantar matsanancin barazanar tsaro.
Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya ƙaddamar a watan Mayu na shekarar 2025 domin dawo da ikon gwamnati a cikin dazuzzuka da ke kara zama mafakar 'yan ta'adda, 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.
An gudanar da bikin yaye ɗaliban a ranar 27 ga Disamba, 2025 a jihohi Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi, inda kowane bangare na horon ya kasance mai tsauri da tsari, domin gina dakaru masu ƙwarewa da jajircewa wajen aikin cikin daji da wuraren da ba a iya shiga cikin sauki.
A bayanin da ya gabatar a bikin yaye su, Mai Ba Da Shawara kan Tsaron Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana shirin a matsayin “mataki mai ƙarfi” wajen dawo da zaman lafiya da kare al’ummomi.
“Wafannan Masu Tsaron Daji ba kawai ma’aikata ba ne da suka sa kaya. Su ne masu kare al’umma, masu tarin bayanai, kuma ginshiki a cikin tsarin tsaronmu. Za su tsaya a ƙasa, su wanke wuraren da masu aikata laifi ke buya, su kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen kwato yankunan da miyagu suka mamaye,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, babu wani tazara tsakanin kammala horo da fara aiki:
“Nan da nan za a tura su bakin aiki, albashinsu da hakkokinsu za su fara nan take.”
An shafe watanni uku ana horar da wadanda aka dauka, inda aka mayar da hankali kan:
Horon jiki da kwakwalwa (physical & mental endurance)
Tsallake cikas, da hanyoyin jure doguwar tafiya cikin daji
Horar da su kan dabarun yaki da tsari na tsaro (tactical drills)
Horo kan mayar da martani yayin farmaki, da kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su
Horon kyakkyawar mu’amala da fararen hula, kare hakkin bil’adama, da bin doka
Daga cikin wadanda suka halarta horon, kashi 98.2 cikin ɗari ne suka kammala. An kori mutane 81 sakamakon kin bin ka’ida, yayin da biyu suka rasu saboda matsalolin lafiya. Mafi yawansu ’yan asalin yankunan da za su yi aiki ne, abin da gwamnati ta ce zai taimaka musu wajen sanin daji, hanyoyin shiga da fita, tare da samun goyon bayan al’umma.
Masu Tsaron Dajin na ƙarƙashin kulawar Ofishin Mai Bada Shawara kan Tsaron Kasa tare da Ma’aikatar Muhalli, karkashin daidaitawar DSS da Hukumar National Park Service. Haka kuma rundunar soji, rundunar sojin ruwan Najeriya, rundunar ’yan sanda da NSCDC duk sun bayar da gudummawa wajen tsari da dabarun aiki.
Gwamnoni da mataimakansu daga jihohin da abin ya shafa sun halarci taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayin da wasu jihohin suka samu wakilci daga mataimakan gwamnoni.
A karshe NSA Nuhu Ribadu ya sake jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da fadada shirin zuwa sauran jihohi:
“Idan muka kare dazukanmu, mun kare kasa. Idan muka kare kasa, mun kare rayukan al’ummanmu. Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba.



No comments