Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Marghi Mazauna Kano Ya Yaba Wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Kan Inganta Tsaro

Daga  Ibrahim Muhammad, Kano  An yaba wa ƙoƙarin Gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf akan jajircewa da yake yi d...


Daga  Ibrahim Muhammad, Kano 

An yaba wa ƙoƙarin Gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf akan jajircewa da yake yi da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a jihar Kano, musamman da ya ƙirƙiro tare da ƙaddamar da jami'an tsaro na Kano, wato 'Neighbourhood Corp' guda 2000, wanda hakan  kyakkyawan hangen nesa ne don kare lafiyar al'umma.

PTIL Elder Wadzani Adamu Sarkin Ƙabilar Marghi  na jihar Kano ne ya yi wannan yabo a lokacin da  abokai da 'yan uwa da al'ummar Marghi suka kai masa ziyarar Barka da Kirsimeti a Fadar sa.

Ya  ce suna gode wa Allah da ya nuna an yin bukukuwa na Christmas cikin kwanciyar lafiya, a wannan karon babu wani abu da ya faru na rashin jin daɗi musamman a jihar Kano.

PTIL Elder Wadzani Adamu ya kuma gode wa  masarautar Kano ƙarƙashin Malam Muhammad Sanusi na Biyu bisa goyon baya da ake ba su. Ya yi fatan za a shiga sabuwar shekara na 2026 cikin zaman lafiya da ci gaba da kyakkyawan dangantaka da ke tsakanin Marghi da al'ummar jihar Kano.

Shi ma a nasa jawabin, ɗaya daga 'yan majalisar  fadar Sarkin na Marghi, Mista Kabilar Zakariya Yusuf Yakub Midala, wakilin Sarkin Fada na Marghi, y a bayyana cew al'ummar Marghi na da kyakkyawanlr dangantaka da al'ummar Kano, shi ya sa ma suka iya harshen Hausa sosai, mafi yawan su suke kuma zaune lafiya tsawon shekaru.

Ya ce su kuma su na zaune ne a cikin al'ummar gari, ba su ware kan su a matsayin wasu ƙabilu na daban ba, su tare suke da al'ummar Kano a kowane yanayi, suna zaune a matsayin 'yan uwa komai ɗaya har da auratayya.

Ya ce Sarkin Marghi na jihar Kano, PTIL Elder Wadzani Adamu  mutum ne mai haƙuri da tausayi da taimako, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi. Domin idan wani abu na buƙata ya taso na taimako, ana tunanin neman mafita sai a ji kawai an ce Elder Wadzani Adamu ya yi ba tare da ya shaida wa kowa ba, wannan an yi sau da yawa da ba za su ƙirgu ba.

Mista Zakariya Yusuf Yakub ya yi kira ga al'ummar Marghi su ci gaba da yi wa wannan masarauta ta Margh da masarautar Kano addu'a kuma al'umma su haɗa kai a riƙa haƙuri da juna, domin rashin haɗin kai da ake samu shi ne ke jawo matsalar tsaro.

Zakariya ya ce idan jama'a suka haɗa kai za a sami zaman lafiya da ƙaruwar arziki a cikin al'umma, a ajiye banbancin yare da na addini, wannan haka Allah ya yi mu, da ya so mu zama yare guda sai ya yi mu haka. Mu dubi abin da ya haɗa mu ya fi abin da ya raba mu yawa.
 

No comments